Babban Sallah: Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tafi Hutu, Ta Sanar Da Ranar Dawowa

Babban Sallah: Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tafi Hutu, Ta Sanar Da Ranar Dawowa

  • Majalisar Dattawan Najeriya za ta tafi hutun babban sallah sai ranar 19 ga watan Yuli za ta dawo
  • Sanata Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan ne ya sanar da haka yayin zamanta na ranar Laraba, ya yi wa yan Najeriya fatan bikin sallah lafiya
  • Lawan ya ce yan majalisar su kasance cikin shiri don za a iya kiransu idan wani batu na gaggawa ya taso koda hutun bai kare ba

FCT Abuja - Majalisar Dattawar Najeriya ta tafi hutun Sallah har sai ranar 19 ga watan Yuli za ta dawo.

Shugaban majalisar dattawan, Sanata Ahmad Lawan ne ya bada sanarwar yayin zaman majalisar na ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Majalisar Dattawan Najeriya.
Majalisar Dattawar Najeriya Ta Tafi Hutun Sallah. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: An ga jinjirin watan Babbar Sallah 1443 a ƙasar Saudiyya

"Ina mana fatan yin hutun babban sallah cikin annashuwa kuma ina taya yan Najeriya murnar bikin sallah.
"Yayin da muke hutu, idan bukatar zaman gaggawa ta taso, mu kasance cikin shiri mu hallara.
"Saboda mu yan majalisa ne, mu ma tamkar likitoci ne a siyasa.
"Mu tabbatar kuma mutanen mazabar mu sun san abin da muke yi a nan.
"Muna da nauyin wayar da kan mutanen da muke yi wa hidima saboda da dama cikinsu ba su san menene ayyukan mu ba," in ji shi.

Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah

A wani rahoton, Kwamishinan ilimi na jihar Kano, ya amince da korar Sabo Muhammad Ahmad, shugaban makarantar sakandiren gwamnati da ke Ɗanbatta (GSS) saboda saɓawa dokar hutun sallah (eid-el-kabir), kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An kori shugaban makarantar ne bayan ya gaza riƙe ɗalibai 300 dake rubuta jarabawar kammala sakandire NECO a makarantarsa duk da umarnin hana ɗaliban tafiya hutun sallah da aka ba shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Hayan Lauyoyi Da Za Kare Ekweremadu Da Matarsa

Kiru ya ƙara da cewa Mr. Ahmad ya baiwa ɗaliban hutu kuma ya tsallake ya tafi mahaifarsa domin yin sallah a can ba tare da sanar da ma'aikatar ilimi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel