Borno: Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji
- Rundunar sojin Najeriya ta bayyana irin aikin da ta yi, ta kuma samu nasara kan 'yan ta'addan Boko haram
- An ruwaito cewa, akalla 'yan Boko Haram 314 sun mika wuya, bayan da sojoji suka kara matsa lambar yakar ta'addanci
- Ya zuwa yanzu, rundunar ta ce tana ci gaba da tantance 'yan ta'addan wadanda wani bidiyo ya nuna lokacin da ake tantance su
Bama, jihar Borno - A yau 29 ga watan Yuni ne rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar karbar akalla 'yan ta'addan Boko Haram 314 da suka mika wuya a karamar hukumar Bamata jihar Borno.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jami'an soji ke ci gaba da matsa lamba ga kakkabe 'yan ta'aadda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
A wata sanarwar da rundunar sojin ta fitar mai dauke da hotuna da bidiyo, an ga lokacin da jami'an ke karbar 'yan ta'addan cikin adadi mai yawa, tare da kokarin tantance su.
Sanarwar da wakilin Legit.ng Hausa ya samo daga shafin Twitter na rundunar sojin Najeriya ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Karin matsin lamba ga yakar ta'addanci da ake ci gaba da yi a yankin Arewa maso Gabas ya sake samun nasara a yau 29 ga watan Yunin 2022 yayin da mayakan Boko Haram/ISWAP 314 suka mika wuya ga sojoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno. Bugu da kari, sojoji sun kuma ceto manoma 12.
"Ana ci gaba da daukar bayanan 'yan ta'addan da suka mika wuya."
Kalli bidiyon:
'Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaron Najeriya, yayin da ake ci gaba da baza wuta a yankin.
2nd Class: Yadda dan fursuna ya gwama zaman kaso da karatun jami'a, kuma ya ba da mamaki
A wani labarin, wani fursuna a gidan gyaran hali na Najeriya da ke Kuje, Mista Chinwendu Heart, ya kammala karatun digiri da sakamako mai kyau (2nd Class) a fannin ilimin Theology daga jami'ar NOUN da ke kan yanar gizo.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Chukwuedo Humphrey ya fitar ranar Laraba a Abuja 29 ga watan Yuni, Punch ta ruwaito.
Humphrey ya ruwaito, NOUN, Dokta Angela Okpala, wacce ta ba da takardar shaidar kammalawar a ranar Talata, inda ta karfafa wa daliban da suka kammala karatun kwarin gwiwar zama jakadun jami’ar nagari da kuma masu kwaazo.
Asali: Legit.ng