Majalisar Dattawa Tana Tantance Ministoci 7 da Buhari ya Mika Sunayensu
- Majalisar Dattawan Najeriya ta fara tantance mutane bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike mata da sunayensu
- 'Yan uwa, abokan arziki da masoyansu sun yi musu rakiya zuwa majalisar inda ake tantancesu domin zama ministocin kasar nan
- A ranar 15 ga watan Yuni ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunayen mutum 7 don maye gurbin ministocin da suka yi murabus
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta fara tantance zababbun sabbin ministoci bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike musu da shi.
Wadanda aka zaban sun samu rakiyar 'yan uwansu, abokan arziki da magoya baya, ana tantance su daya bayan daya a yayin zaman majalisar, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari a wasikar da ya aike a ranar 15 ga watan Yunin 2022, ya bukaci majalisar da ta tabbatar da su a matsayin sabbin ministocin da zasu maye gurbin bakwai da suka yi murabus.
Yace an mika bukatar tabbatar dasu ne a karkashin sashi na 147, sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka gyara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka zaban sune: Henry Ikechukwu Iko daga jihar Abia, Umana Ikon Umana daga jihar Akwai Ibom; Ekumankama Joseph Nkama daga jihar Ebonyi da Goodluck Nanah Opiah daga jihar Imo.
Sauran sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub daga jihar Kano; Ademola Adewole Adegoroye daga jihar Ondo da kuma Odum Udi daga jihar Ribas.
Majalisar Dattawa ta Aike Wakilai UK Kan Kamen Sanata Ekweremadu
A wani labari na daban, majalisar dattawa ta ce zata tura wakilanta zuwa Burtaniya don ganin halin da tsohon mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekwdremadu, wanda ake tuhumarsa da yunkurin cire sassan jikin yaro a Turai.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan ranar Laraba bayan majalisar dattawan ta fito daga ganawar sirri, wanda ya dauki tsawon awa guda.
'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai
Lawan ya ce wakilan, wadanda suka hada da 'yan kwamtin kula da lamurran waje na majalisar dattawan zasu je birnin London ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng