Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Sake Zuwa Kotu Da Kayan 'Bokaye'

Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Sake Zuwa Kotu Da Kayan 'Bokaye'

  • Kotu ta ki sauraron Malcolm Omirhobo, lauya mai kare hakkin bil adama da ya bayyana a babban kotun tarayya a Legas
  • Mai shari'a Tijani Ringim ya bukaci dage sauraron karar yana mai cewa sai an tabbatar ko doka ta bawa Omirhobo damar zuwa kotu da irin wannan shigar
  • Omirhhobo ya fara yin wannan shigar na masu addinin gargajiya zuwa kotu ne bayan hukuncin kotun koli da ta halastawa mata musulmi sanya hijabi a makarantun gwamnati

Legas - Lauya mai kare hakkin bil adama, Malcolm Omirhobo, ya bayyana gaban alkali a babban kotun tarayya da ke Legas a ranar Litinin sanye da tufafi irin na gargajiya.

Mr Omirhobo ya daura mayafi mai launin ja a kugunsa, sarkuna na gargajiya a wuyansa da kuma tufafin lauya.

Malcom Omirhhobo
Alkali Ya Ki Sauraron Lauya Mai Addinin Gargajiya Da Ya Tafi Kotu Sanye Da Kayan 'Bokaye'. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Ya bayyana da irin wannan shigar a kotun koli a makon da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yanke shawarar yin wannan shigar ne biyo bayan hukuncin kotun koli na halastawa dalibai mata sanya hijabi a makarantun gwamnati a Legas.

Lauyan, dan asalin Jihar Delta, ya bayyana tufafinsa a matsayin irin shigar da masu bautan Olokun ke sanya wa.

An tattaro cewa takwarorinsa a Legas sunyi ta kallonsa suna murmushi kafin fara sauraron shari'ar.

Kotu bata saurari Omirhobo ba

Lauyan ya bayyana a gaban mai shari'a Tijani Ringim kan wasu sharia biyu amma alkalin ya bukaci ya bayyana dalilin da yasa ya yi wannan shigan.

"Ba za ka iya bayyana a gaban kotu a matsayinka na kwararre da irin wannan shigar ba," The Cable ta rahoto alkalin ya ce.
"Zan dage cigaba da sauraron karar ka kuma sai ka dawo ka bayyana a kotu idan doka ta baka damar zuwa kotu a haka."

Kara karanta wannan

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

Mr Ringim ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba.

Bayan Halasta Saka Hijabi, Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Tafi Kotun Koli Sanye Da Tufafin Bokaye

Tunda farko, kun ji cewa Lauya mai kare hakkin bil adama, Malcolm Omoirhobo, a ranar Alhamis ya kwashi yan kallo saboda irin tufafin da ya saka yayin zuwa kotun koli a Abuja, rahoton The Punch.

Hotunan da aka yada a dandalin sada zumunta sun nuna Omoirhobo sanya da tufafin lauya hade da wasu abubuwa da suka yi kama da na masu maganin gargajiya ko bokaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164