Gwamnatin Buhari ta gamu da sabon tasgaro a hanya wajen binciken Bukola Saraki

Gwamnatin Buhari ta gamu da sabon tasgaro a hanya wajen binciken Bukola Saraki

  • A farkon makon nan ne aka samu labari lauyoyin hukumar EFCC sun koma kotu da Bukola Saraki
  • Wannan karo ma ba a dace ba domin Alkali Inyang Ekwo da ya kamata ya saurari karar bai zo ba
  • A dalilin haka aka sake daga shari’ar sai Oktoba, za ayi kusan wata shida kenan kotu ba ta zauna ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A ranar Litinin, 27 ga watan Yuni 2022, aka zauna a kotu da nufin a cigaba da sauraron karar hukumar EFCC ta kasa da kuma Bukola Saraki.

Hukumar dillacin labarai ta kasa ta ce ba a iya cigaba da wannan shari’a ba domin Alkalin da ya kamata ya saurari karar bai iya zuwa kotu a ranar ba.

An shirya cewa Mai shari’a Inyang Ekwo zai saurari shari’ar a matsayin kara na biyar da na shida da ke gabansa a ranar, amma kuma hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

A dalilin haka ne kotu ta sake daga wannan shari’a zuwa 5 ga watan Oktoba. Hakan yana nufin sai bayan fiye da watanni uku za a sake sauraron shari’ar.

An kuma...

Kafin zaman da aka nemi ayi na ranar Litinin, sai da lauyoyin hukumar EFCC suka shafe tsawon watanni biyu su na jiran a hadu a gaban kotun tarayyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai shari’a Inyang Ekwo ya daga karar a watan Mayun 2022 ne bayan Lauyoyin Bukola Saraki da sauran wadanda ake zargi sun ki halartar zaman kotu.

Bukola Saraki
Bukola Saraki a wajen taron PDP
Asali: UGC

Baya ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki, ana tuhumar Babban lauyan gwamnati, Sufeta Janar na ‘yan sanda, jami’ar DSS a wannan kara.

Wadanda suka shigar da karar su ne Lauyoyin hukumar ICPC ta kasa da na hukumar nan ta CCB.

Kamar yadda The Eagle ta fitar da rahoto, Alkalin yana wajen wani taro da ya shafi aikinsa a ranar Litinin da aka yi niyyar za a ji hukunci da za a yanke.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Yadda aka fara shari’a tun 2019

EFCC ta na kokarin binciken kudin da Saraki ya samu a lokacin yana gwamna a jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011, har ta fara karbe masa wani gidansa.

Amma tsohon ‘dan majalisar ya shigar da kara har biyu a Mayun 2019 a gaban Alkali Taiwo Taiwo, yana kalubalantar taba masa dukiya da hukumar ta yi.

Saraki ya ci nasara a kan EFCC, amma daga baya aka maida shari’a gaban Anwuli Chikere. Bayan Alkalin ya yi ritaya kwanakin baya, sai karar ta zo wajen Ekwo.

Tsohon CJN zai samu N2.5bn

Dazu aka ji labari Tanko Ibrahim Muhammad GCON zai tafi da Biliyoyin kudi, baya ga katafaren gida da Gwamnati za ta gina masa a Birnin Tarayya Abuja.

A dokar Najeriya, an ware makudan kudin sallaman da ake biyan duk wani Alkalin Alkalai na kasa idan aikinsa ya zo karshe, haka majalisar NJC ta yi tanadi.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban alkalan Najeriya Tanko Muhammad

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng