Da duminsa: 'Yan ta'adda sun harba 1 daga cikin fasinjojin jirgin Abj-Kd dake wurinsu

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun harba 1 daga cikin fasinjojin jirgin Abj-Kd dake wurinsu

  • 'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun harba daya daga cikin fasinjojinj dake hannunsu
  • Kamar yadda Tukur Mamu ya bayyana, fasinjan mai suna Mohammad Al-Amin yana cikin mawuyacin hali a yanzu haka
  • Ya bayyana cewa, ta yuwu hakan sun yi ne domin aikewa da sako ga gwamnatin tarayya kan cewa komai zai iya faruwa da fasinjojin

'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jrigin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris sun harba daya daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su.

Kamar yadda Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald wanda shi ke jagorantar sasanci da 'yan ta'addan yace, wanda suka harban mai suna Mohammed Al-Amin yana cikin mawuyacin hali.

Labari da duminsa
Da duminsa: 'Yan ta'adda sun harba 1 daga cikin fasinjojin jirgin Abj-Kd dake wurinsu
Asali: Original

Mamu, wanda ya jagoranci sakin fasinjoji 11 daga cikin wadanda aka sace, ya tabbatar da wannan cigaban ga jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jarumin dan kwallo Ahmad Musa ya rabawa mata 5000 kudi Naira milyan 100

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zan iya tabbatar muku cewa an harbi fasinja daya daga cikin wadanda aka sace kuma bayanin daga majiya mai karfi ne. Zai yuwu da gangan ne saboda su aiko da sako. Kashe wadanda suka sace abu ne da muka san zasu iya. Sun yi barazanar yin hakan tuntuni," yace.

Yace gwamnati dole ne ta shirya daukar alhaki idan aka ki daukan mataki a kan lokaci.

Mamu yace akwai yadda suke samun bayanai amma har yanzu gwamnati ta ki daukan mataki a kai.

"Na san irin rikicin dake tattare da wannan lamarin, hakan yasa nake ta jaddada cewa dole ne shugaban kasa muhammadu Buhari ya shirya daukar wasu matakai da doka bata aminta da su ba idan yana son ceto rayukan jama'ar nan," yace.
“A kan nasarar da muka samu, mun bude wata dama ne wacce gwamnati daga nan take da karfin kawo karshen lamarin cikin kwanaki uku zuwa hudu.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo Nijeria bayan halartan taron CHOGM 2022 a Kigali

“Ina tabbatar da cewa za mu iya idan mun samu hadin kansu da goyon bayansu, kuma idan bai faru ba idan da gwamnati ta yo abinda ya dace, zan amince in kuma dauka nauyi. Lamurran gaggawa irin wannan basu bukatar sanya mara amfani."

Buhari ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta tabbatar da an ceto rayukan wadanda lamarin ya ritsa da su.

Kaduna: 'Yan Ta'addan Ansaru Sun Kwace Wasu Yankuna, Sun Haramta Harkokin Siyasa

A wani labari na daban, 'yan ta'addan kungiyar Ansaru sun haramta duk wasu lamurran siyasa a yankuna masu tarin yawa na gabashin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda Kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari ta bayyana.

Isahq Kasai, shugaban kungiyar ciganan masarautar Birnin Gwari, BEPU, wanda ya bayyana hakan, yace kungiyar akai-akai take daukar matasan yankin aiki tare da aurar da yara mata kananan a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Justice Olukayode Ariwoola zai zama sabon Alkalin Alkalai

Kwamitin ta kara da bayyana yadda kungiyar ta cigaba da samun karbuwa daga jama'an anguwanni musamman a tsohuwar Kuyello da Damari na gundumar Kazage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel