Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo Nijeria bayan halartan taron CHOGM 2022 a Kigali

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo Nijeria bayan halartan taron CHOGM 2022 a Kigali

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar Kigali, Kasar Rwanda kuma ya dira a birnin tarayya Abuja ranar Lahadi.

A baya mun rahoto cewa Shugaban kasan a ranar Laraba 22 ga watan Yuni ya bar Nijeria ya tafi kasar Rwanda domin halartan taron kasashen rainon Ingila wato common wealth wanda ya gudana daga ranar 22 zuwa 26 ga watan Yunin 2022.

Taron na CHOGM 2022, Wanda wasu shugabannin suka halarta, an mishi take da 'samar da saukakken gaba': hadaka da kawo sababbin sauye sauye ya ta'allaka ne akan cigaba ga mutane miliyan 2 da suke rayuwa a kasashe masu yancin kansu a nahiyar Afrika, Asiya, Amerika, da Europe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel