Jarumin dan kwallo Ahmad Musa ya rabawa mata 5000 kudi Naira milyan 100

Jarumin dan kwallo Ahmad Musa ya rabawa mata 5000 kudi Naira milyan 100

  • Kamar yadda ya saba duk lokacin da ya dawo gida hutu, Ahmed Musa ya yiwa zaurawa tara mai kyau
  • Musa ya kashe naira milyan dari wajen rabawa mata dubu biyar naira dubu ashirin-ashirin
  • A cewarsa, wannan shine taimakon da zai iya yiwa mutane cikin irin halin da al’umma ke ciki

Plateau - Kyaftin na yan kwallon Super Eagles, Ahmad Musa, ya rabawa mata zaurawa da marasa karfi dubu biyar (5000) kudi Naira milyan dari (100m) a garin Jos.

Mr Williams Gyang, Daya daga cikinnp hadiman Ahmad Musa, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a Jos.

Gyang yace Ahmed Musa ya sake wannan rabo kamar yadda ya saba don rage radadin talaucin da jama’a.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: Sanata ya tona asirin wasu gwamnonin APC da suka dagula tsarin APC

Musa wanda ya rabawa matan kowacce N20,000 ya bayyana cewa babu ruwan yunwa da addinin ko kabila saboda haka ba’ayi la’akari da bangaranci wajen rabon ba.

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Matsin tattalin arzikin da mutane ke fama da shi na da yawa sosai kuma wannan ne dan karamin kokarin da zanyi don taimakawa zaurawa da marasa karfi.”
Ahmed Musa
Jarumin dan kwallo Ahmad Musa ya rabawa mata 5000 kudi Naira milyan 100
Asali: Getty Images

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel