Masha Allah: Malami Daga Kudu Ya Fassara Kur'ani Zuwa Harshen Igbo, Za A Kaddamar A Ranar Juma'a

Masha Allah: Malami Daga Kudu Ya Fassara Kur'ani Zuwa Harshen Igbo, Za A Kaddamar A Ranar Juma'a

  • Wata kungiyar musulmi ƙarƙashin Malam Muhammad Chukwuemeka ta yi nasarar fassara Kur'ani mai Girma zuwa harshen Igbo don amfanin yan uwa musulmi a yankin kudu maso gabashin Najeriya
  • Mal Chukwuemeka ya ce za a kaddamar da Kur'anin fassarar harshen Igbo a ranar Juma'a a Abuja, ya kuma yi kira ga yan uwa musulmi su bada tallafi don a buga kwafi masu yawa a yaɗa a kudu
  • A cewar Malam Chukwuemeka, ya shafe a ƙalla shekaru biyar yana aikin fassarar Al-Kur'ani mai girman kafin ya kammala

FCT, Abuja - Wata kungiyar musulmi daga kudu maso gabashin Najeriya za ta kaddamar da Kur'ani mai girma da aka fassara zuwa harshen Igbo a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai

Wakilan kungiyar karkashin kungiyar 'Igbo Muslims Da'awah' karkashin jagorancin Mal Muhammad Muritala Chukwuemeka ta bayyana hakan a jiya yayin ziyara da suka kai hedkwatan Daily Trust a Abuja.

Mal Chukwuemeka.
Za A Kaddamar Da Kur'ani Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo a Kudancin Najeriya A Ranar Juma'a. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana yayin ziyarar Mal Chukwuemeka ya ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar yada sakon Allah ga yan uwansu Igbo ta hanyar amfani da kur'anin da aka fassara.

Malam Chukwuemeka, dan asalin karkashin karamar hukumar Orlu ta Jihar Imo ya ce, Musulunci addini ne na zaman lafiya kuma ya hana kashe mutane.

Ya bayyana cewa ya shafe shekaru biyar kafin ya kammala fassarar.

A birnin tarayya Abuja za a kaddamar da Kur'anin da aka fassara zuwa harshen Igbo

Malamin haifafan Imo, amma, ya yi kira ga yan Najeriya su hallarci kaddamarwar da za a yi bayan sallah Juma'a a masallacin Ansar-ud-deen da ke Maitama a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya maye gurbin kwamishinoni 19 da ya tsige daga muƙamansu

Ya yi kira ga yan Najeriya su bada taimako domin a buga kwafi masu yawa don yadda kalmar Allah (SWT) ga Igbo a kudu maso gabas da sauran sassan Najeriya.

"Na shafe a kalla shekaru biyar kafin kammala fasarar. Muna kira ga yan Najeriya su taimaka a wallafa kwafi masu yawa na littafin mai tsarki. A yanzu, mun wallafa kwafi 500, mun aika da kwafi 100 zuwa kudu maso gabas," in ji shi.

Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana, Jihohin Borno Da Adamawa Sun Samu Rangwame

A wani rahoton, Hukumar kula da jin dadin alhazai, NAHCON, ta sanar da kudaden kujerun hajji na bana. Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta yi la'akari dukkan lamuran da suka shafi aikin hajjin.

Hajiya Fatima Sanda, shugaban sashin hulda da jama'a na hukumar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164