Da Duminsa: Buhari ya Gwangwaje Tsohon CJN Tanko da Lambar Yabo Mafi Daraja ta 2 a Najeriya

Da Duminsa: Buhari ya Gwangwaje Tsohon CJN Tanko da Lambar Yabo Mafi Daraja ta 2 a Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gwangwaje tsohon babban alkalin Najeriya, Muhammad Tanko, da lambar yabo ta GCON
  • Kamar yadda aka gano, wannan lambar yabo ta Grand Commander of the Order of Niger, ita ce mafi daraja ta biyu da za a iya bai wa 'dan Najeriya
  • Buhari ya bayyanaa cewa, Tanko yayi aiki tukuru tare da dogaro da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya gwangwaje tsohon shugaban alkalan Najeriya, Muhammad Tanko da lambar yabo Grand Commander of the Order of Niger, GCON.

Lambar yabon ita ce mafi daraja ta biyu a lambobin karramawa da za a iya bai wa 'dan kasar Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa da ya Kamata a Sani Game da Sabon CJN Olukayode

CJN Muhammad Tanko
Da Duminsa: Buhari ya Gwangwaje Tsohon CJN Tanko da Lambar Yabo Mafi Daraja ta 2 a Najeriya
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana bada lambar yabon a yayin rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya a gidan gwamnati dake Abuja.

A yayin jawabi a taron, Buhari ya ce an bada lambar yabon ga alkalin ne sakamakon aiki mai kyau da yayi yayin da yake karagar shugaban alkalan Najeriya.

Ya zuba kalaman yabo kan Tanko, wanda yayi murabus sakamakon fama da rashin lafiyan da yake yi.

Ya kara da cewa a karkashin kulawar mai shari’a Muhammad, bangaren shari’a na yin amfani da karfin da ya dace daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999.

Hotuna: Jastis Olukayode Ya Karba Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN

A wani labari na daban, Justis Olukayode Ariwoola na kotun koli ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jastis Olukayode Ya Karba Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rantsar da Justis Ariwoola a yayin wani biki da aka gudanar a zauren majalisa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ariwoola mai shekaru 62 a duniya ya karbi aiki daga wajen tsohon shugaban alkalan kasar, Justis Tanko Muhammad. Zai ci gaba da rikon kwarya har zuwa lokacin da majalisar alkalan kasa za ta tabbatar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel