Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

  • Mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammad ya yi murabus daga mukaminsa na babban jojin Najeriya CJN
  • Babban masanin shari'a na kasa, Tanko Muhammad ya yi murabus ne a daren Lahadi, 26 ga watan Yuni, bisa dalilan rashin lafiya
  • Dangane da wannan lamari da aka samu, Legit.ng ta tattaro wasu manyan dalilan da watakila suka kai ga yin murabus dinsa

A yau ne aka tashi da labari mai daukar hankali, babban jojin Najeriya, mai shari'a Tanko Muhammad ya yi murabus.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mai shari’a Muhammad ya yi murabus ne a daren Lahadi, 26 ga watan Yuni, inda ya bayyana dalilin haka da rashin lafiya.

Dalilai masu karfi da suka sa CJN ya yi murbasu daga kujerarsa
Rashawa?, manyan dalilai biyar da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Channels TV ta ruwaito cewa ana ci gaba da shirye-shiryen rantsar da sabon babban jojin kasar, wanda ya fi kowa mukami a kotun kolin kasar; mai shari'a Olukayode Ariwoola a matsayin jojin kasa na rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Hadimin alkali: Babban dalilin da yasa shugaban alkalan Najeriya ya yi murabus

Ko da yake ba a ba da sanarwar nada Ariwoola a hukumance ba, amma ana kyautata zaton shi ne mafi girma da zai rike mukamin, bisa al'adar aikin shari'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya zuwa murabus dinsa, rahotanni sun nuna cewa Mai Shari’a Muhammad na fama da matsanancin rashin lafiya.

Manyan dalilan da suka sa ya yi murabus kamar yadda wasu fusatattun alkalai suka bayyana

A kwanakin baya ne dai alkalan kotun kolin su 14 suka rubuta masa wasika domin nuna rashin jin dadinsu game da yadda al’amura ke gudana a kotun koli.

1. Rike aiki sakaka

A cikin wasikar da aka kai masa, alkalan sun zargi babban jojin na Najeriya da kin magance matsalolin halin ko-in-kula da aiki duk da cewa sun ja hankalinsa game da hakan.

2. Rashin masauki da ababen hawa

Fusatattun alkalan sun kuma koka da rashin matsuguni da ababen hawa a kotunan su.

Kara karanta wannan

Hotunan dan autan marigayi sarkin Kano Ado Bayero yayin da ya angwance da mata biyu a lokaci guda

3. Hana alkalai samun tallafin balaguro zuwa kasashen waje

Alkalan sun ci gaba da bayyana zarginsu kan jojin da cin duniyarsa da tsinke tare da da matarsa da ‘ya’yansa da ma’aikatansa, amma su ya hana su tafiya da mataimaka a tafiye-tafiyen kasashen waje.

4. Rashin mataimakan bincike na shari'a

Fusatattun alkalan sun yi tir da rashin samar musu da mataimaka masu binciken shari'a, duk da girman shari'ar da ake yankewa a kotunansu.

5. Rashin wadatar wutar lantarki

Dangane da matsalar samar da wutar lantarki, alkalan sun ce an tsare su su yi aiki daga karfe 8 na safe zuwa karfe 4 na rana a kullum, saboda rashin man diesel na janareta bayan da babbar magatakardar kotun koli, Hajo Bello ta sanar da su hakan.

A bangare guda, Mai shari’a Tanko Muhammed bai halarci bude taron horas da alkalai kan yadda za a warware rigingimu da cibiyar shari’a ta kasa ta shirya ba, a daidai lokacin da aka samu rahoton murabus din, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An tono shekarun yaron da Sanata Ekweremadu suka kai Ingila domin cire masa koda

Ko da yake babu wani alkalin kotun koli da ya halarci taron, ko menene dalili?

Buhari ya Gwangwaje Tsohon CJN Tanko da Lambar Yabo Mafi Daraja ta 2 a Najeriya

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya gwangwaje tsohon shugaban alkalan Najeriya, Muhammad Tanko da lambar yabo Grand Commander of the Order of Niger, GCON.

Lambar yabon ita ce mafi daraja ta biyu a lambobin karramawa da za a iya bai wa 'dan kasar Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana bada lambar yabon a yayin rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya a gidan gwamnati dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.