Warware batu: FG ta yi bayani game da karyata ta da ASUU ta yi kan zaman sulhu

Warware batu: FG ta yi bayani game da karyata ta da ASUU ta yi kan zaman sulhu

  • Gwamnatin Najeriya ta magantu kan batun da ke yawo cewa, ma'aikatar kwadago ta yi karya a batun gayyatar ASUU zaman tattaunawa
  • A wata sanarwar da ma'ajkatar kwadago ta fitar, an bayyana dalla-dalla yadda batun yake tare da yin karin haske kan shirin gwamnati na gaba
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar malaman jami'o'i ASUU kan batun alawus da albashi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya ta yi karin haske kan rashin gayyatar kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) taron da aka yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa.

Rahotanni sun karade kafafen yada labarai a makon da ya gabata, inda aka ruwaito Ministan kwadago, Chris Ngige yana cewa hukumomin da yaji ya shafa za su gudanar da wani taro kan dakile yajin aikin malaman jami'a.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Yadda batun gayyata taro ya hada ASUU da FG fada
Warware batu: Yadda batun gayyatar taron tattaunawa gwamnati da ASUU ta kasance | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai, shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels ya ce kungiyar tasa bata samu goron gayyata daga gwamnatin tarayya ba domin halartar taron, lamarin da ya tunzura gwamnati.

Yadda batun yake

Wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Mista Olajide Oshundun ya fitar ta bayyana cewa taron an yi shi ne da ma’aikatan ma’aikatu da kwamitocin hukumomin gwamnatin tarayya ne kawai kuma babu wata kungiyar jami'a da aka gayyata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani yankin sanarwar ya bayyana wadanda aka gayyata da cewa:

"Taron dai an yi shi ne ga ma’aikatu da kwamitocin hukumomin gwamnatin tarayya da suka hada da ma’aikatar ilimi ta tarayya, ma’aikatar kudi ta tarayya, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, ofishin kasafin kudi na tarayya, hukumar kula da albashi, kudade da kudi da ma’aikata (NSIWC), ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA)."

Kara karanta wannan

ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

Sanarwar ta ce, an kira taron ne domin tantance irin ci gaban da aka samu kawo yanzu wajen magance dambarwar da ke tsakanin ma'aikatar da kuma kungiyoyin da ke yajin aiki.

Hakazalika, ma'aikatar ta kuma yi bayanin shirinta na tattaunawa da ASUU a nan gaba bisa la'akari da rahoto da bayanan da kwamitin ya fitar, ta ce:

"Bayan samun bayanai daga bangaren gwamnati ne ma’aikatar kwadago za ta zauna da dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da kungiyoyin kwadago kan teburin tattaunawa domin duba yarjejeniyar kafin sanya hannu ko amincewa.
"Don haka duk zage-zagen cewa Ma’aikatar Kwadago ba ta tausayawa dalibai, kungiyoyi da iyaye, wanda Minista na daya daga ciki, to a yi watsi da su.
"Ministan ya sha samun yabo daga shugabannin kungiyar ta ASUU bisa rawar da ya taka wajen warware matsalar da ta addabi fannin ilimi."

ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

Kara karanta wannan

FG Tana Gayyatar Kwararrun Ma'aikatan Gwamnati Da Su Nemi Gurbin Akanta Janar

A tun farko kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'in, ASUU, tace gwamnatin tarayya bata gayyaceta wani taro ba a ranar Alhamis.

A ranar Laraba da ta gabata, Chris Ngige, ministan kwadago da aikin yi, yace gwamnatin tarayya nan babu dadewa za ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta tsunduma watanni hudu da suka gabata.

Ya kara da cewa, matsalolin bangaren biyan albashi da salon da gwamnatin tarayya ta zo da shi wanda kungiyar bata aminta da shi ba duk za a shawo kan shi a taron da za ta yi da kungiyar a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.