Kaduna: 'Yan Ta'addan Ansaru Sun Kwace Wasu Yankuna, Sun Haramta Harkokin Siyasa
- 'Yan ta'addan kungiyar Ansaru a jihar Kaduna sun kwace wasu yankunan karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar inda suke cin karensu babu babbaka
- Kamar yadda masarautar Birnin Gwari ta bayyana, kungiyar ta dage wurin daukan matasan yankin aiki tare da aurar da kananan yara mata
- Ya sanar da yadda kungiyar miyagun ta haramta dukkan tarukan siyasa a yankin kuma take daukar matakai wanda gwamnati ta kasa yin komai a kai
Birnin Gwari, Kaduna - 'Yan ta'addan kungiyar Ansaru sun haramta duk wasu lamurran siyasa a yankuna masu tarin yawa na gabashin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda Kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari ta bayyana.
Isahq Kasai, shugaban kungiyar ciganan masarautar Birnin Gwari, BEPU, wanda ya bayyana hakan, yace kungiyar akai-akai take daukar matasan yankin aiki tare da aurar da yara mata kananan a yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamitin ta kara da bayyana yadda kungiyar ta cigaba da samun karbuwa daga jama'an anguwanni musamman a tsohuwar Kuyello da Damari na gundumar Kazage.
"Ko a wannan makon, an sa ranar auran mambobin kungiyar biyu da yara mata biyu sannan za a yi daurin auren wannan Asabar din mai zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Angwayen Ansaru sun gindaya wasu dokoki game da bikin. Sun kafa sharadin cewa bayan bikin zasu tafi da amaren daji sannan su yi rayuwa a can tare dasu kuma basa bukatar amaren su tafi da kayan daki in banda kwanukan cin abinci, kuloli da katifu saboda duk wani abu baya ga wadannan ba za su amince dasu ba."
BEPU ta bayyana cikin alhini yadda mazauna yankin da suka shiga kungiyar ke tsoron zama cikin garin saboda fargabar kada 'yan sanda ko jami'an tsaro su kama su, jaridar Leadership ta ruwaito.
"A halin yanzu kungiyar ta'addancin Ansaru na yawo kwararo-kwararo sun saba kyautar memori ga mazauna yankin wanda ya kunshi abun da suka yi imani da shi da kuma akidarsu.
"Abun da yafi tada hankali shi ne yadda kungiyar ta haramta duk wasu lamurran siyasa a yankuna da dama irin su Damarin gundumar Kazage. 'Yan siyasar wadannan anguwanni sai sun je wasu anguwanni da ke makwabtaka da su kafin su iya gudanar da taron siyasa.
"Misali, wannan makon, an ga wani 'dan acaba da ke zaune anguwar Makera na Kazage da fostar wani 'dan takara majalisar jihar Kaduna, hakan yasa Ansaru suka nada masa dukan kawo wuka.
"Yanzu mutanen wadannan anguwanni suna matukar kyara gami da tsanar shiga lamurran siyasa. Bamu san yadda wannan zaben mai zuwa zai kasance ba a wadannan yankunan saboda ba a samu damar yin zaben karamar hukumar da ya gabata a yankin ba duba da tsananin rashin tsaro wanda yasa aka bayyana sakamakon zaben ba tare da an kammala ba.
"A takaice, kungiyar ta'addancin Ansaru na cigaba da samun mabiya a yankuna da dama. Sune ke tare mutane tare da fadar abun da suke so a yi a kauyuka, suna cin karensu ba babbaka.
"Daga cikin mazauna yankin da ke da ra'ayin shiga kungiyar kullum kara yawa suke. Wadanda suka riga suka shiga suna zuwa yankuna don su dauki wadanda ke da ra'ayi zuwa dajika don suyi kwanaki ana horar dasu a kan akidar. Idan suka dawo, suna yawan fadi cewa, mambobin Ansaru na cr musu suje su tayasu yakar gwamnati da siyasa don su mai da jihar ta musulunci.
"Lamarin na ci mana tuwo a kwarya duk da irin mummunan abun da ke faru, babu wani kwakwaran mataki da hukumomi suka dauka. Ko cikin kwanakin nan da aka kai wa mutanenmu hari gami da babbaka motoci takwas bayan tarin jama'an da aka yi garkuwa dasu kan titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna, babu abun da gwamnati ta yi. Gwamnati bata taba nuna damuwarta game da lamarin ko ta jajantawa yankin mu ba.
"An kai hare-hare yankunan mu, garkuwa da mutane da halaka su a kullum ba tare da gwamanati ta yi martani ko nuna damuwa ba. Saboda haka muna kiran gwamnati da ta jami'an tsaron ta wajen kai samame a mabuya wadannan hatsabiban a dajikanmu don dakile ayyukansu gami da yin garanbawul ga kashe-kashen da suke yi a kullum" a cewarsa.
Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna jihar da su dauka makamai tare da bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga.
A yayin da korafi kan tabarbarewar tsaro ta yawaita a jihar, hukumomin Zamfara sun umarci kwamishinan 'yan sandan jihar sa ya bada lasisin rike bindigu ga wadanda suka dace su rike a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin tace a shirye take da ta tabbatar da jama'a sun samu makamai ballantana manoma, domin bai wa kansu kariya.
Asali: Legit.ng