Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

  • Rundunar sojin Najeriya, wacce ta kunsa sojin saman NAF uku da jiragen yaki sun tarwatsa a kalla sansanin 'yan ta'addan bakwai a jihar Kaduna a ranar Laraba
  • Haka zalika, an gano yadda dakarun suka sheke 'yan bindiga 23 yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200 gami da kona gidaje a yankin Danya na jihar Zamfara
  • Har ila yau, dakarun sun halaka a kalla wasu 17 da ake zargin 'yan ta'adda ne gami da tarwatsa baburansu da kwale-kwale a jihar Neja bayan tabbatar da hatsabibai ne

Dakarun sojin saman Najeriya sun budewa tawaga biyu ta masu satar shanu yayin da suka kai wani samame a Jihar Zamfara da Neja wuta ta jiagen yaki.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

Haka zalika, dakarun, tare da soji uku na saman Najeriya (NAF), jiragen yaki da jiragen bindigu sun kai samame ga 'yan ta'addan a jihar Kaduna gami da tarwatsa sansanin su a ranar Laraba.

Jiargen NAF
Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani jami'in binciken sirri na sojin, wanda ke daya daga cikin wadanda suka kai samamen Zamfara, ya bayyana yadda aka sheke 'yan ta'adda 20 a wurin Kofar Danya na jihar, yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200.

Majiyar ta bayyana yadda, "Ba tare da bata lokaci ba, biyu daga cikin mayakan jirgin saman NAF suka yi dirar mikiya a tsakiyar tawagar 'yan ta'addan gami da bude musu wuta yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200 a Kofar Danya na jihar zamfara.
"A lokacin da suka isa wurin, tawagar sun hango 'yan ta'addan masu tarin yawa kan babura, suna kokarin shiga kauyuka gami da sace shanu.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

"Ba tare da zato ko tsammani ba, jiragen yakin suka budewa 'yan ta'addan wuta tare da dasa abubuwa masu fashewa, gami da halaka 'yan ta'adda 23 bayan wadanda suka samu raunuka."

A dayan bangaren, PRNigeria ta gano yadda a daren Laraba, dakarun soji suka yi ido biyu da babura dauke da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne inda suka doshi wani wajen kwale-kwale kusa da tafkin Shiroro cikin Neja.

"An ga wasu kalilan daga cikin mutane suna jira a wannan wajen hawa kwale-kwale, inda aka lura da yadda suke isa gami da tare fasinjoji tare da makamai.
"Bayan tabbatar da mutanen 'yan ta'adda ne da mabiyansu, hakan yasa aka yi masu luguden wuta, wanda ya yi sanadiyar sheke 'yan ta'adda 17 gami da tarwatsa baburansu da kwale-kwalensu," a cewar wani jami'in tsaron yankin.

Kamar yadda wani jami'in tsaro a Kaduna ya bayyana, jiragen yakin sojin sun yi lebur din a kalla sansanin 'yan ta'adda bakwai a dajin Ukambi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng