Yanzu-Yanzu: Nan Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG

Yanzu-Yanzu: Nan Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, nan babu dadewa daliban Najeriya zasu koma ajujuwansu domin cigaba da karatu
  • Kamar yadda Sanata Ngige, ministan kwadago da aikin yi ya bayyana yayin taron FEC, a halin yanzu ana hango karshen yajin aiki
  • Ya musanta zargin da ake ta yadawa kan cewa gwamnatin tarayya na kokarin kawo wani sabon salon biyan ma'aikatan albashinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ana dab da komawa karatu nan babu dadewa saboda yadda ta mayar da hankali wurin shawo kan matsalolin kungiyoyin jami'o'i.

Kungiyar malaman jami'o'i msau koyawa, ASUU, Kungiyar ma'aikatan jami'o'in da basu koyarwa, NASU da Kungiyar Manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU duk suna yajin aiki.

Yanzu-Yanzu: Nan Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG
Yanzu-Yanzu: Nan Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin jawabi a taron majalisar zartarwa ta tarayya, FEC wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa dake Abuja, ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya ce ana hangon karshen yajin aikin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Ministan wanda ya musanta zargin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya na shirin samar da wani sabon salo na biyan kungiyoyin, yace gwamnatin ta yi kira ga cibiyoyin, har da NITDA domin ta yi bayani kan nasarar da aka samu kan abinda ya kawo yajin aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ngige yayin jawabi, yace gwamnatin tarayya tana da burin ganin dalibai sun koma makaranta, Daily Trust ta ruwaito.

Yace taron ranar Alhamis ana tsammanin zai duba rahoton cigaba wanda cibiyoyin da ke kula da rikicin da suka hada da NITDA kan yadda ake ciki a bangaren gwajin ingancin UTAS wanda ASUU ke son a yi mata amfani da shi tare da U3PS wanda SSANU da NASU ke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel