Shugaba Buhari ya yi wa Obasanjo shagube, yace ba zai nemi ya sake zarcewa a mulki ba

Shugaba Buhari ya yi wa Obasanjo shagube, yace ba zai nemi ya sake zarcewa a mulki ba

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da Boris Johnson a wajen taron CHOGM da ake yi a Kigali
  • Firayim Ministan Birtaniya ya tambayi Muhammadu Buhari ko zai sake neman takara a Najeriya
  • Shugaban kasar ya nuna cewa ya ci taliyar karshe, ya yi habaici ga wanda ya taba neman yin haka

Rwanda - Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba zai nemi karin wa’adi idan lokacinsa ya cika ba, ya jaddada barinsa mulki a 2023.

Da yake jawabi a wajen taron CHOGM na kasashen renon Birtaniya da ake yi a Kigiali, kasar Rwanda, Muhammadu Buhari ya ce ya gama yin takara.

Daily Trust ta rahoto Buhari a tattaunawarsa da Firayin Ministan Birtaniya, Boris Johnson yana cewa wanda ya nemi ya zarce a karo na uku bai ji dadi ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya shiga yawon ganin ido gidan tarihin kisan 'kare dangi na Ruwanda

Boris Johnson ya tambayi shugaban Najeriyan ko zai nemi ya sake takarar shugaban kasa. A amsar, ya yi wata magana da bai ambaci sunan wani ba.

Da ya tashi bada amsa, Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wata magana mai harshen dabo, wanda ta sa wadanda suke wurin, suka fashe da dariya.

Wanda ya jarraba bai ji dadi ba

“In nemi wani wa’adin? A’a! Wanda ya fara yunkurin hakan bai ji dadi sosai ba.” - Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari
Tawagar Muhammadu Buhari a Kigali Hoto: @buhari.sallau
Asali: Facebook

Shari'ar Mazi Nnamdi Kanu

Jaridar ta ke cewa shugaba Buhari ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa an hana jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu damar ganawa da lauyoyinsa.

A wani jawabi da shugaban kasar ya fitar ta hannun Femi Adesina, ya tabbatar da cewa an ba Kanu hakkinsa duk da irin cin mutuncin da ya yi wa Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

“Kanu ya yi ta fadar maganganun banza a game da Najeriya a lokacin da yake Birtaniya, a lokacin da aka kama shi, sai mu ka maka shi a kotu.”

“Sai ya kare duk abubuwan da ya fada a can. Lauyoyinsa su na haduwa da shi. Idan za a tuna, ya taba tserewa, za mu tabbata bai sake yin haka ba.”

- Femi Adesina

Har ila yau, Buhari wanda ya rage masa kasa da shekara guda ya bar mulki, ya yi bayanin irin kokarin da gwamnatinsa ta ke yi a kan matsalar rashin tsaro.

Zaben 2023

Ku na sane cewa Atiku Abubakar ya na ikirarin ya yi arziki ne tun a gidan kwastam, shi ma Bola Tinubu yana cewa kafin ya shiga siyasa ya zama Attajiri.

Amma a 1993 an taba kai Bola Tinubu kotu bisa zargin alaka da kudin harkar kwayoyi. Sannan an taba zargin Atiku Abubakar da boye $40m a kasar Amurka

Kara karanta wannan

Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng