Buhari ya shiga yawon ganin ido gidan tarihin kisan 'kare dangi na Ruwanda

Buhari ya shiga yawon ganin ido gidan tarihin kisan 'kare dangi na Ruwanda

  • Gabanin halartan taron da ya kai shi Rwanda, shugaba Buhari ya fita ziyara gidan tarihi a Kigali
  • Shugaban kasan ya ziyarci gidan tarihin kisan 'kare dangi da ya faru a kasar inda aka kashe mutum sama da 250,000
  • Shugaba Buhari ya dira birnin Kigali, kasar Ruwanda da yammacin Laraba tare da mukarrabansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kigali - Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar yawon ganin ido gidan tarihin kisan kare dangi na kasar Ruwanda da ya auku kimanin shekaru 29 da suka gabata.

Shugaban kasan ya kai ziyarar ne ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni, 2022.

A dakin tarihin, Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su rike hakuri da juna su koyi zama da juna lafiya.

Buhari ya yi yawo cikin gidan tarihin kuma ya ziyarci makabartar da aka kashe sama da mutum 250,000.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

kigali
Buhari ya shiga yawon ganin ido gidan tarihin kisan 'kare dangi na Ruwanda Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bisa jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin.

Gabanin kammala ziyararsa, Buhari ya rubuta cewa:

"Muna tunawa da wadanda aka kashe a kisar 'kare dangin Rwanda, muna addu'a kada irin wannan abu na mugunta da zalunci ya sake faruwa a tarihi saboda kabila, ko addini."
"Najeriya na shirye da hana faruwar irin wannan abu a duniya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel