Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

  • Tsagerun yan bindiga sun kai hari kan al'ummar yankin Rahamawa da Shagari low-cost a jihar Katsina
  • Maharan sun kuma sace mazauna yankin da dama kafin jami'an tsaro suka dakile yunkurinsu na tafiya da su
  • Sai dai babu tabbacin ko sun yi nasarar tafiya da wasu ko kuma jami'an tsaron sun ceto dukkanin mutanen

Katsina - A ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki gidajen da ke yankin Rahamawa da Shagari low-cost a jihar Katsina.

Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna yankin da ba a san adadinsu ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wata majiya a karamar hukumar Jibia wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa an gano maharan da tsakar rana suna tisa keyar mutanen da suka sace zuwa inda suka ajiye baburansu.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

Tswirar Katsina
Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A safiyar nan, da misalin karfe 6:15 na safe mutanenmu sun hango yan bindigar suna tisa keyar mutanen da suka sace sannan mun ji cewa sun fito ne daga yankin Rahamawa da ke Katsina.
“Mutanenmu sun bayyana cewa sun ga maharan kimanin su 13 zuwa 15 suna tafiya cikin sauri tare da mutanen da suka sato.”

Sai dai kuma ya ce an yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro wadanda suka tarwatsa maharan sannan suka ceto mutanen, yana mai cewa bai da tabbacin ko dukka mutanen da aka sace ne aka ceto.

Wani dan kungiyar yan banga a garin da abun ya faru wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an yan sanda sun gaggauta bin sahun maharanidon ceto mutanen da aka sace.

Ya ce:

“Da gaske ne yan ta’adda sun kawo farmaki a safiyar nan. Mun samu bayanai kan shige da ficensu kuma mun yi masu kwanton bauna a hanyarsu tare da sauran jami’an tsaro, amma ga mamakinmu, mun kasa gano inda suka lafe.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa da Mutane Sun ci mu Tarar N1m Saboda Lattin Kai Kudin Fansa, Mata da Miji

“Mun bar yankin da misalin karfe 4:00 na asuba kawai sai muka gano cewa sun kai farmaki garuruwan da ke kusa da Shagari Low-cost. Yanzu haka da nake magana da ku, wata tawaga ta sojoji, yan sanda da yan banga suna bibiyarsu ciki harda jirgi mai tashi da saukar ungulu daga rundunar sojojin sama."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Daily Trust ta kuma rahoto cewa da yake tabbatar da harin, kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce maharan sun farmaki gidan wani Abdullahi Esha, dan kasuwa a kwatas din Sokoto Rima da ke garin Katsina. Sun shiga gidan ta shingen da ke tsakani sannan suka sace diyarsa.

Isah ya ce:

“A jiya 22/06/2022 da misalin karfe 0230 na safe ‘yan ta’adda dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari gidan wani Abdullahi Esha dake unguwar Sokoto Rima Katsina sannan suka yi garkuwa da ‘yarsa mai shekaru 18.

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

“Nan take aka tura ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane da ‘yan sintiri yankin inda suka fatattaki ‘yan bindigar. Tawagar dai sun yi artabu da 'yan ta'addar lamarin da ya sa suka gudu.
"Daga baya, rundunar ta yi nasarar ceto wanda abin ya shafa, wata Walida Abdulaziz Maigoro, 'yar shekara 18, ba tare da ta jin rauni ba."

Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa a kalla mutane uku ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka bindige har lahira a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.

Vanguard ta kuma rahoto cewa an bindige wani mutumin a kafa yayin da yan bindigan sun sace wata mata mai suna Hawau Yusuf mai zaune a Unguwan Makera.

Wani mazaunin garin, Marwan Zayyana, wanda ya tabbatarwa Vanguard lamarin, ya ce maharan sun kai hari garin ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, a kan babura, suka rika cin karansu ba babbaka har 4.30 a garin.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng