'Yan fashi sun mamaye lambun shakatawa a Abuja, sun tashi hankalin 'yan hutu
- 'Yan fashi da makami sun farmaki wani lambun shakatawa a babban birnin tarayya Abuja lokacin da masu hutu ke tsaka da jin dadinsu
- Maharan wadanda suka dungi harbi kan mai uwa da wahabi sun yiwa masu shakatawa a wajen fashin kudi da kayayyaki masu muhimmanci
- Sai dai an bayyana cewa babu wanda ya jikkata a yayin harin, inda yan fashin suka bar wajen cikin gaggawa
Abuja - Wasu ‘yan fashi da makami sun farmaki wani lambun shakatawa na Aco Estate Garden da ke kan hanyar filin jirgin sama a Abuja inda suka yiwa wadanda suka je shakatawa fashin kudade da kayayyakinsu, Daily Trust ta rahoto.
Wani mazaunin yankin, Ezenwa Alfred, ya ce yan fashin wadanda yawansu ya kai shida sun farmaki lambun ne a gefen hedkwatar kungiyar NUT, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin sannan suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin suka yiwa mutane fashi.
Ya ce:
“Ina hanyar barin lambun zuwa gidana bayan na amsa kira cewa nayi bako. Na yi tafiyar wasu yan mita kadan kawai sai na fara jin karar harbi.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yan mintuna bayan nan sai aka fada masa cewa yan fashi da makami sun farmaki lambun sannan sun yiwa wadanda suka je shakatawa fashi.
Wani da abun ya faru kan idonsa da aka bayyana da Samuel, ya ce yan fashin sun fito daga wata mota yar mita kadan daga wajen masu hutun sannan suka taka har zuwa mashigin lambun kafin suka farmake su, shafin Linda Ikeji ya rawaito.
Ya ce:
“A zahiri ma, daya daga cikin yan fashin ya fara zuwa kamar zai siya lemun kwalba. Ba a dade ba sai na fara jin karar harbi, na tsere ne ta kofar baya.”
Sai dai ya ce babu wanda ya jikkata a yayin harin, inda yace yan fashin sun tsere nan take.
Ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan birnin tarayya kan lamarin ba.
Katsina: Yan Sanda Da Yan Bijilante Sun Aike Da Wasu Yan Ta'adda Barzahu Bayan Tafka Gumurzu
A wani labarin, tawagar hadin gwiwa da ta kunshi rundunar yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina sun kashe yan ta'adda biyu yayin musayar wuta a kauyen Sabon Dawa.
A cewar kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, ya ce an yi musayar wutan ne a yammacin ranar Talata, rahoton The Punch.
Asali: Legit.ng