Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada cewa za a ladabtar da 'yan ta'adda masu kai farmaki kan 'yan Najeriya da basu ji ba, basu gani ba
- A cewar shugaban kasan, makiyan kasar nan ne kuma azzalumai, ragwaye wadanda suke son ganin rabewar kan kasar nan ta hanyar cuso rikicin addini
- Shugaban kasan ya ce yayi matukar alfahari tare da sha'awar yadda 'yan Najeriya suka dinga zuwa kai gudumawar jini ga wadanda harin Owo na jihar Ondo ya ritsa dasu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace masu kai farmakin kwanakin nan kan cocina "ragwaye" ne kuma za a ladabtar da su kan laifukansu.
A makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun kai farmaki cocin Katolika dake Owo a jihar Ondo inda suka halaka mutum 40.
Har ila yau, mutane uku sun rasa rayukansu a ranar Lahadi, sakamakon farmakin da 'yan bindinga suka kai wasu coci biyu a jihar Kaduna.
Kamar yadda wata takardar ranar Laraba da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, Buhari yace farmakin duk aikin azzaluman mutane ne wadanda ke kokarin ganin sun rura wutar rikicin addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasan yace makiyan Najeriya ne ke son tarwatsa ta saboda 'yancin addinai, banbancinmu shi ne yasa kasar ta zama gagaruma. Banbancinmu ne yake kara wa kasar karfi.
"Ba za mu bar su ba. Hankalin kasar ba zai dauke ko ya rabu ba sakamakon wadannan shiryayyun hari wadanda duk siyasa take kawo su," Buhari yace.
"Masu harin matsorata ne, basu da karfi kuma azzaluman mutane ne da bindigan suke kashe mutanen da basu da makamai a wuraren bauta."
Buhari yace ganin 'yan Najeriya suna tseren zuwa bada kyautar jini ga wadanda harin Owo ya ritsa dasu ya birgeshi.
Ya kara da kira ga 'yan Najeriya kan kada su dubi addinai, su hade kai kuma yayi wa iyalan wadanda lamarin ya shafa addu'a.
"A game da ragwayen, za a ladabtar da su kan laifukansu. Za mu tabbatar an yi adalci. Ku tabbatar cewa jami'an tsaro sun shiga lamarin," yace.
Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi
A wani labari na daban, bayan kwanaki 85 da sacesu a harin jirgin kasan Abuja/Kaduna, Shugaba Muhammau Buhari ya umurci jami'an tsaro su ceto sama da mutum 50 da suka rage hannun yan bindiga.
Legit ta kawo muku cewa a ranar 28 ga Maris, 2022, wasu yan bindiga sun kai farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda suka hallaka akalla mutum 8, suka jikkata goma kuma sukayi awon gaba da mutum 62.
Bayan kimanin watanni uku, Shugaba Buhari ya bayyana cewa wajibi ne a ceto wadanda ke hannun yan bindiga da ransu.
Asali: Legit.ng