Yahoo Boy: Kotu Ta Yanke Wa Abdulhakeem Hukuncin Wanke Banɗaki Na Wata 8 a Osun

Yahoo Boy: Kotu Ta Yanke Wa Abdulhakeem Hukuncin Wanke Banɗaki Na Wata 8 a Osun

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi nasara a kotu bayan gurfanar da wasu dalibai kan zargin aikata damfara ta intanet
  • An yanke wa wani cikin wadanda aka gurfanar a kotun hukuncin wanke ban ɗaki na tsawon wata takwas bayan ya amsa laifinsa
  • Amusa Abdulhakeem Oluwasegunfunmi, wanda aka yanke wa hukuncin dalibi ne na ajin ƙarshe a Jami'ar Tai Solarin, Ijebu Ode Jihar Osun

Jihar Osun - Hukumar Yaki da Rashawa Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati, EFCC, ta yi nasara bayan gurfanar da wasu mutane biyar a kotunan tarayya da manyan kotun jiha a Ibadan, Jihar Oyo da Osogbo, Jihar Osun.

Dan Damfara Ta Intanet a Osun.
Damfara Ta Intanet: Yahoo Boy, Abdulhakeem, Zai Wanke Banɗaki Na Wata 8 a Osun. Hoto: @OfficialEFCC.
Asali: Twitter

Daya daga cikin wadanda aka samu da laifin shine Amusa Abdulhakeem Oluwasegunfunmi, dalibin ajin ƙarshe a Jami'ar Tai Solarin, Ijebu Ode, Jihar Ogun, wanda aka yanke wa watanni takwas ya wanke ban ɗaki saboda yin sojan gona da nufin aikata damfara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun sako tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro da wasu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zai wanke ban daki na tsawon watanni takwas kamar yadda hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter.

Sauran sun hada da Ajisafe Sofia Olaide, Lawal Samuel Morenikeji, Osuolale Abdullahi, Osuolale Abdullahi Abiodun, da Olamilekan Ridwan Taofeek.

An same su da aikata laifuka daban-daban masu alaka da zamba ta Intanet.

Sun amsa laifin da hukumar ta EFCC ta gurfanar da su a gaban kotu kan zargin aikatawa.

An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa

A wani rahoton, Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari kawo mutum 7 majalisa don su maye gurbin wasu ministocinsa

Ya ce an mika batun ga sashin hukunta masu laifi a jami'ar kuma aka amince da rage wa malaman da abin ya shafa mukami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel