Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

  • Majalisar dattawa ta yi sabbn nade-nade, inda ta samu sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar
  • Wannan na zuwa ne tun bayan da wanda ke kan kujerar ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai adawa
  • A wasikar da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karba, an bayyana sunayen mutum biyu da aka nada

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta nada Sanata Philip Tenimu Aduda (FCT) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar, The Nation ta ruwaito.

Haka kuma an nada Sanata Chukwuka Utazi a matsayin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya sanar da nadin yayin da yake karanta wasiku daban-daban guda biyu dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu.

Kara karanta wannan

APC ta sake rasa Sanata da wasu Jiga-jigan ‘Yan siyasa zuwa NNPP a jihar Bauchi

Majalisar dattawa ta yi sabbin nade-nade
Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye ta zama babu kowa a kanta tun bayan ficewar Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu) daga PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi, inji Punch.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Jamil Gulma, wanda ya tabbatar da sauya shekar ya fitar da sanarwa.

Vanguard ta ruwaito shi yana cewa:

“Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba domin shelanta shiga jam’iyyar PDP, kuma zai nuna sha’awar sa ta tsayawa takarar kujerar a yanzu.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

Ka zabi daya daga cikinmu: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari

A wani labarin, 'yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas sun rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), domin bai wa yankin Kudu maso Gabas damar fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

A wani kwafin wasikar da wakilin Punch ya samu a ranar Talata, ‘yan takarar sun bukaci Buhari ya sa baki a yayin zaben domin samar da “shugaba mai kyau”.

Wasikar na dauke da sa hannun Ikeobasi Mokelu, tsohon ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Dokta Ogbonnaya Onu; karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da Mrs. Ken Uju-Ohanenye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.