Da gangan na fita daga gidanmu: Ameerah Sufyan ta nemi afuwar jama’a kan kitsa garkuwa da kanta da ta yi

Da gangan na fita daga gidanmu: Ameerah Sufyan ta nemi afuwar jama’a kan kitsa garkuwa da kanta da ta yi

  • Ameerah Sufyan, budurwar da ta kitsa labarin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da ita a shafin Twitter ta fito ta bayar da hakuri
  • A wata wallafa da ta yi a shafinta a yau Litinin, 20 ga watan Yuni, Ameerah ta ce da gangan ta fita daga gidansu sannan ta kai kanta jeji tare da horar kanta da yunwa
  • Ta bayyana cewa rashin hankali da mugun tunani ne suka kai ta ga aikata haka, inda ta nemi a taya ta da addu'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Matashiyar budurwa, Ameerah Sufyan wacce ta yi zargin cewa an yi garkuwa da ita a shafin Twitter a makon da ya gabata ta fito ta bayar da hakuri a kan kitsa lamarin da ta yi da kanta.

Da farko mun ji cewa Ameerah ta je shafin Twitter inda ta yi zargin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da ita da wasu mutane 16 a yankuna daban-daban na Abuja.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

Sai dai kuma, rundunar yan sandan birnin tarayya wacce ta gano matashiyar kwanaki uku bayan ta yi kokawar ta karyata ikirarin cewa an sace ta ne.

Yan sanda da matashiyar budurwa
Da gangan na fita daga gidanmu: Ameerah Sufyan ta nemi afuwar jama’a kan kitsa garkuwa da kanta da ta yi Hoto: @Ameerah_sufyan
Asali: Twitter

Da take bayar da hakuri a wata wallafa da ta yi a shafin Twitter a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, Ameerah ta bayyana cewa lamarin ya afkune sakamakon rashin hankalinta da tunani mara kyau a zuciyarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma mika godiyarta ga jami’an rundunar yan sandan Najeriya kan namijin kokarin da suka yi a kanta sannan ta bukaci jama’a da su taya ta da addu’a.

Ta rubuta a shafin nata:

“Barka da yau jama’a, ina so na ba jama’a, sashin yan sanda gaba daya da yan uwa da abokan arziki hakuri kan batar da su da nayi da wannan wallafa da nayi a Twitter. Babu abu makamancin wannan da ya faru kuma duk rashin hankalina da tunani mara kyau ne.

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba

“Ina kuma son mika godiyata ga IG da CP Babaji Sunday kan taimakona da suka yi kan wannan. Allah ya saka muku da alkhairi.”
“Da gangan na fita daga gidanmu, na je wadannan wurare, na shiga dazuzzuka sannan na horar da kaina da yunwa da kishiruwa na tsawon kwanaki hudu haka kawai. Babu batun garkuwa da ni, babu abun da ya faru. Ina mai bayar da hakuri kuma dan Allah ku tayani da addu’a. ina bukatarsa.

An gano Ameerah da tayi ikirarin ‘Yan bindiga sun shiga Abuja, sun yi garkuwa da su 17

A baya mun ji cewa rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun yi nasarar gano Ameerah Sufiyanu, wata Baiwar Allah da tayi ikirarin an yi garkuwa da ita a ranar Talata.

A ranar 14 ga watan Yuni 2022, Ameerah Sufiyanu ta shaidawa Duniya cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ram da ita, tare da wasu mutane 17 a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

'Dan Allah ta ya zan samu Saurayi?' Wata kyakkyawar budurwa ta koka da zaman kaɗaici

Tun lokacin aka shiga neman inda aka kai ta domin kuwa ta iya bayyana inda ta ke da halin da su ke ciki. Budurwar tayi wannan ne ta shafinta na Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng