Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30
- Bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu a coci, sun nemi a tara makudan miliyoyi domin sako jama'ar
- Wannan na zuwa ne ta bakin shugaban yankin da 'yan bindigan suka sako, wanda yana daya daga cikin wadanda aka sace
- Ya kuma bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya ce sun yi tafiyar tazara mai tsawo kafin isar su mafakar 'yan ta'addan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Shugaban Angwan Fada da ke kauyen Rubu inda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jama'ar coci a ranar Lahadi, Elisha Mari ya fita daga hannunsu kuma sun nemi ya tara Naira miliyan 100 domin a sako mutanensa.
Elisha Mari wanda yana daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin bayan da masu garkuwan suka sako shi, rahoton Vanguard.
Rahotanni a baya sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai hari cocin Maranatha Baptist da cocin St Moses Catholic da ke Robuh, Ungwan Aku, karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar Lahadi; inda aka kashe mutanen yankin uku tare da sace sama da 30.
An ce ‘yan bindigan sun mamaye yankin ne a kan babura kusan 30, kowanne yana dauke da ‘yan bindiga biyu zuwa uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake zantawa da manema labarai a lokacin da shugabannin hukumomin tsaro da tawagar gwamnatin jihar Kaduna suka ziyarci yankin a ranar Litinin, Elisha Mari ya ce ‘yan bindigan sun far wa kauyukansu inda suka rika harbe-harbe tare da sace mutanensa.
Yadda aka dafi da mutanen
Ya ce sun kwashe kusan awanni biyu ana tafiya a cikin dajin kafin su isa ga mafakar masu garkuwa da mutanen.
A cewarsa:
“An sake ni ne saboda ni ne shugaban gargajiyan yankin amma sun ce in tara akalla Naira miliyan 100 kudin fansa kafin a sako wadanda aka yi garkuwa da su.”
Wani mazaunin yankin, Bashir Usman, ya ce mutane uku da ‘yan bindigan suka kashe a harin na ranar Lahadi, lokacin da suka yi yunkurin kalubalantar ‘yan ta’addan.
Al’ummar yankin na cikin fargaba kuma har yanzu ba a koma daidai ba, duk da cewa jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a yankin da abin ya shafa da kewaye.
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36
A wani labarin, akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna ranar Lahadi.
Mazauna kauyukan ne suka bayyana hakan a wata ganawa da jami’an tsaro a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.
Mazauna yankin sun ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwarsu, domin ba za su iya zuwa gonakinsu ba a halin yanzu don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.
Asali: Legit.ng