Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

  • Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, an kwantar da tsohon shugaban Najeriya a asibitin Landan bisa wani rashin lafiya
  • Sai dai, an ruwaito cewa, an sallame shi bayan samun sauki daga jinyar da aka boye wa duniya tun farko
  • Hadimin Buhari kan harkokin yada labarai ne ya bayyana abin da ya faru yayin daya wallafa batun ziyartar shugaban

An sallami wani tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda aka kwantar a asibitin birnin Landan saboda rashin lafiyar da ba a san ko wane iri ba.

Leadership a ruwaito cewa, ‘yan uwa da mataimakansa ne suka boye batun zaman Janar Abdulsalami a asibiti.

An kwantar da tsohon shugaban Najeriya a asibiti
Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Amma, mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyanawa jama'a halin lafiyar tsohon shugaban kasar a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HML din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa

Shehu, wanda ya rubuta a shafinsa na Facebook, ya ce ya ziyarci Janar Abdulsalami a Landan kuma ba ya cikin wani hali mai tsanani a yanzu, don haka babu wata fargaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hadimin na shugaban kasa Buhari ya rubuta a shafinsa cewa:

"Mun godewa Allah bisa rahamarsa. Yanzu na kammala ziyartar Mai Girma Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa. An sallame shi a asibiti a wani gida da ke Landan kuma da alama ba ya cikin wani mummunan yanayi.
"Ya kasance cikin raha, yana mai nuna sha'awar abubuwan da ke faruwa a gida Najeriya. Don Allah, babu wata damuwa."

Janar Abdussalami Abubakar na daya daga cikin masu fada a ji a Najeriya, kuma cikin wadanda mulkinsu ya yi matukar tasiri ga Najeriya.

An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kwankwaso ya zabi Barista Ladipo Johnson matsayin mataimakinsa

A wani labarin, a ranar Lahadi ne wasu ‘yan daba suka far ma motar bas din da ke dauke da ma’aikatan ofishin gwamnan jihar Legas a tsakanin Ebute-Ero da Adeniji, na yankin Iga-Iduganran a Legas, inda ‘yan jarida akalla biyu suka samu raunuka, wasu kuma suka kuje a jikinsu.

'Yan daba sun afkawa 'yan jaridan ne da ke cikin ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Tribune Online ta ruwaito.

An rahoto cewa, tsagerun sun kuma jefi motocin da ke cikin ayarin da ya kunshi jiga-jigan siyasa ciki har da Gwamna Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje; da sauran wadanda suka bar fadar Oba na Legas, Oba Rilwanu Akiolu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.