Da Dumi-Ɗumi: Yan bindiga sun kai hari har cikin Masarauta, sun sace Sarki a jihar Arewa

Da Dumi-Ɗumi: Yan bindiga sun kai hari har cikin Masarauta, sun sace Sarki a jihar Arewa

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa har cikin fadar Basaraken Panyam, sun yi awon gaba da shi ranar Litinin a jihar Filato
  • Wasu bayanai daga mazaunin yankin sun bayyana cewa mazauna garin sun yi yunkurin kai ɗauki amma maharan suka buɗe wuta don tsorata su
  • Har yanzun hukumar yan sanda reshen Filato bata ce komai ba duk da mutane sun kai rahoton lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Miyagun yan bindiga 20, sun yi awon gaba da Basaraken gargajiya a jihar Filato, Mai Martaba Aminu Derwan, yayin da suka kai hari fadarsa da ke Panyam, ƙaramar hukumar Mangu.

Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun sace Derwan, babban basaraken Panyam, bayan sun tsorata mutane da harbe-harben bindiga a safiyar Litinin.

Wani mazaunin yankin Panyam, Moses Garuba, ya tabbatar da sace Basaraken ga jaridar Punch a Jos, babban birnin jihar Filato ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara, rai ya salwanta

Mahara sun sace Basarake a Filato.
Da Dumi-Ɗumi: Yan bindiga sun kai hari har cikin Masarauta, sun sace Sarki a jihar Arewa Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Garuba ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A jiya da tsakar dare wasu yan bindiga da suka haura 20 ɗauke da manyan makamai suka kewaye fadar Basaraken da ke Panyam saboda gidansa ba'a katange yake ba."
"Wasu da suka gane baƙin fuska sun zagaye gidan Basaraken sai suka ankarar da sauran mazauna gari da ƙararrawa, amma da maharan suka ji ƙarar sai suka buɗe wuta sannan suka tafi da Basaraken."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Wasu mazauna yankin waɗan da suka fusata da harin sun bayyana cewa tuni suka kai rahoton abinda ya auku Ofishin yan sanda na garin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Filato, Alabo Alfred, domin jin halin da ake ciki ba'a same shi ba, kasancewar wayarsa ta salula na kashe.

Wannan harin da sace Basaraken shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren garkuwa da masu rike da Sarauta a jihar Filato da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Bauchi, sun aikata ɓarna sun sace Basarake da ɗansa

A ranar Lahadi ta makon da ya gabata, yan bindiga suka sace Malamin Majami'a, Rabaran James Kantoma a yankin ƙaramar hukumar Jos ta gabas da kuma wani Basarake, Ugoh Ababs.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari karamar hukumar gwamnan Bauchi

Yan bindiga sun kai harin yankin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi, arewa mas o gabashin Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun sun yi yunkurin sace mutane amma suka fuskanci turjiya daga matasa dole suka tsere daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel