Yan bindiga sun sake kai hari Jihar Bauchi, sun sace Basarake da ɗansa

Yan bindiga sun sake kai hari Jihar Bauchi, sun sace Basarake da ɗansa

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai hari jihar Bauchi kwanaki kaɗan bayan harin da wasu suka kai yankin ƙaramar hukumar Alkaleri
  • Maharan sun yi awon gaba da Dagacin kauyen Zira, ƙaramar hukumar Toro, Yahaya Saleh Abubakar da ɗan sa guda ɗaya
  • Hukumar yan sanda ta sanar da cewa ta tashi tawagar bincike da wasu dakarun yan sanda sun bazama neman su

Bauchi - Yan bindiga su farmaki ƙauyen Zira da ke ƙaramar hukumar Toro, jihar Bauchi, inda suka yi awon gaba da Dagacin garin, Yahaya Saleh Abubakar, da ɗansa, Habibu Saleh.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ruwayar Daily Trust.

Ya ce ƴan bindigan sun shiga ƙauyen wanda ke ƙarƙashin Caji Ofis ɗin Rsihi kuma mai iyaka da jihar Filato, da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara, rai ya salwanta

Mahara sun sake shiga jihar Bauchi.
Yan bindiga sun sake kai hari Jihar Bauchi, sun sace Basarake da ɗansa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa kwamishinan yan sanda na jiha, Umar Mamman Sanda, ya umarci DPOn yankin ya bazama aikin ceto mutanen da aka sace ba tare da sun cutu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tribune Online ta ruwaito Wikil ya ce:

"Tuni hukumar yan sanda ta tashi tawagar bincike da wasu jami'an yan sanda domin kuɓutar da mutanen da aka sace. A halin yanzu jami'an mu sun bazama sun mamaye cikin jeji suna binciken mutanen."
"Muna tabbatar wa mazauna wannan ƙauye cewa nan ba da jimawa ba zasu ga dawowar waɗan da aka sace."

Ya kuma roki ɗaukacin al'umma su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da harkokin su na yau da kullum, kana su kai wa yan sanda rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari har cikin Masarauta, sun sace Mai Martaba Sarki a Arewa

Ko maharan sun nemi kuɗin fansa?

Hakimin Leme, Alhaji Aliyu Yakubu Leme, ya bayyana cewa har yanzun maharan ba su tuntuɓi iyalan Dagacin ba domin jin abinda suke buƙata.

Wannan harin garkuwan na zuwa ne kwanaki biyar bayan yan bindiga sun farmaƙi wasu yankuna a ƙaramar hukumar Alkaleri, inda mutum huɗu suka rasa rayukansu, wasu uku suka jikkata.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa lamarin tsaro na cigaba da taɓarɓarewa a yankin.

Ya ce yan bindigan na shigowa ne daga jihohin da ke makwaftaka da Bauchi musamman waɗan da suka haɗa iyakar dazuka kamar jihar Taraba.

Mutumin ya ce:

"Tsaro ƙara lalacewa yaƙe a Bauchi, an fara ɗaukar masu rike da saraita, a iya fahimta ta gwamnatin mu ta Bauchi na iya bakin kokarinta."

A wani labarin kuma Wani mutumi ya fara tattaki da ƙafa daga Bauchi zuwa Legas don kaunar Tinubu a 2023

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari karamar hukumar gwamnan Bauchi

Yayin da gangar siyasa ke cigaba da kaɗawa mutane na kokarin nuna goyon bayan su ga ƴan takara ta hanya daban-daban.

Wani mai suna Usman Adamu ya isa Kafanchan dake Kaduna, ya taso daga Bauchi zuwa Legas don nuna kaunarsa ga takarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel