Ba kudi suka sa muka ba Ganduje Sarauta ba, Sarkin kasar Ibadan

Ba kudi suka sa muka ba Ganduje Sarauta ba, Sarkin kasar Ibadan

  • Sarkin Ibadan, Oba Lekan Balogun, Alli Okunmade ll ya magantu a kan nadin sarautar da aka yiwa Gwamna Abdullahi Ganduje da matarsa a kasarsu
  • Oba Lekan Balogun ya bayyana cewa ba kudi ne suka sanya su baiwa gwamnan Kanon da iyalinsa sarauta ba
  • A ranar Asabar, 18 ga watan Yuni ne aka nada Ganduje a matsayin Aare Fiwajoye ita kuma Hafsat aka nada ta sarautar Aare Fiwajoye

Oyo - Sarkin kasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, Alli Okunmade ll a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, ya ce masarautar bata siyar da sarauta imma na gargajiya ko na karramawa.

Yayin da yake jawabi a wajen nadin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da matarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje a matsayin Aare Fiwajoye da Yeye Aare Fiwajoye na kasar Ibadan, ya bayyana cewa ba kudi ne yasa aka basu sarautar ba.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Abdullahi Ganduje tare da matarsa
Ba kudi suka sa muka ba Ganduje Sarauta ba, Sarkin kasar Ibadan Hoto: Oluyole FM
Asali: Facebook

Leadership ta rahoto cewa yayin da yake bayyana cewa taron shine irinsa na farko a karkashin wannan mulki, Olubadan ya ce:

“Abubuwan da suka sanya aka zabe su, za ku yarda da zabin. Ina son na saka shi a tarihi, amma dan uwanmu, Sarkin Yarbawan Kano, Alhaji Injiniya Muritala Alimi Otisese (Adetimirin-1) ya ketare hanyoyin da wasu sarakunan yau basu ketare ba. Wannan dan uwan namu ne, wanda shima dan kasa ne ya gabatar da ma’auratan na Kano zuwa fadar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Daga sarkin Yarbawan Kano, mun gano yadda gwamna na jihar Kano tare da matarsa basu da kabilanci. An fahimtar da mu yadda bakinmu suka tallafawa takara da bayyanar dan uwanmu a matsayin Sarkin Yarbawan Kano kimanin shekaru biyu da suka wuce.
“Mutum mai son zaman lafiya, Mai girma, Dr. Ganduje, shine ya zo Ibadan lokacin da aka samu rikici tsakanin yan kasuwa Hausawa da mutanen Sasa a kasuwar Sasa a wancan lokacin dan kwantar da tarzoma da dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

“Tsohon dalibin jami’ar Ibadan, a halin yanzu sabon Aare Fiwajoye yana gina dakin taro na Jami’ar, aikin da aka ce an kammala kashi 70 cikin dari.
“Bugu da kari, idan daya daga cikin Karin maganar Yarbawa ya bayyana cewa duk wanda ya bayar da auren da ko yarsa yana da tarin ayyukan alkhairi, toh Ganduje kansancewarsu surukai a Ibadan ta hanyar yarsu da ta auri danmu, Idris Ajimobi sun yi mana komai.”

Hotuna: Tinubu Da Wasu Manyan Kasa Sun Halarci Nadin Sarautar Ganduje Da Gwaggo a Ibadan

A baya mun kawo cewa a ranar sabar 18 ga watan Yuni ne aka nada gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Farfesa Haftsat Ganduje sarauta a masarautar Ibadan.

Mai martaba Olubadan na Ibadan, Dr Lekan Balogun ya nada Ganduje sarautar Aare Fiwajoye ita kuma Hafsat aka nada ta sarautar Aare Fiwajoye, rahoton Leadership.

Wasu manyan mutane a Najeriya sun samu halartar nadin sarautar cikinsu har da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2022 kuma jagoran jam'iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng