Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai kazamin hari ƙaramar hukumar gwamna Bauchi
- Yan bindiga sun kai harin yankin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi, arewa maso gabashin Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun sun yi yunkurin sace mutane amma suka fuskanci turjiya daga matasa dole suka tsere daji
- Wasu majiyoyi sun ce ganin ba zasu samu abin da suka nufa ba, yan bindigan sun buɗe wa matasan wuta
Bauchi - Miyagun yan bindiga da ake zaton yan fashin daji ne sun kai kazamin hari ƙaramar hukumar Alkaleri, da ke jihar Bauchi, inda suka kashe mutum hudu, wasu uku suka jikkata.
Jaridar Punch ta tattaro cewa gwamnan Bauchi, Bala Muhammed. ya fito ne daga yankin ƙaramar hukumar ta Alkaleri.
Wasu majiyoyi daga yankin da suka haɗa da jami'an tsaro sun bayyana cewa lokacin da yan bindigan suka kai hari Tudun Wadan Jada, wanda mutane suka fi sani da Jimari Jauro-Bano da nufin sace mutane, an ankarar da mutane.
Matasan ƙauyen da wasu daga kauyukan da ke kewaye suka haɗa kan su suka tunkari maharan, hakan ya sa yan bindigan suka gaza tafiya da mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma da maharan suka ga ba zasu cimma kudirin su ba sai suka buɗe wa matasan wuta, nan take hudu suka mutu yayin da wasu uku suka ji munanan raunuka.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai da sharaɗin ɓoye sunansa cewa:
"Maharan sun shigo kauyen da misalin ƙarfe 11:45 na daren ranar Alhamis, sun shigo a mashina, da mutane suka farga sai suka buɗe wuta, sannan suka tsere daji. Bisa rashin sa'a mutum huɗu suka mutu, wasu uku suka jikkata."
Yace an gaggauta kai waɗan sa suka jikkata wani Asibiti a jihar Gombe, jihar da take kusa da Bauchi.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Shugaban ƙaramar hukumar, Yusuf Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida ranar Jumu'a, inda ya ce maharan sun shiga sabuwar Tudun Wadan Jada da nufin sace mutane, da mutane suka farga sai suka tsere.
Ya ce yan bindiga sun shiga yankin ta dazukan dake da iyaka da Taraba, Gombe da Filato. Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun bazama domin kamo su.
Garba ya ƙara da cewa sun gudanar da taron tsaro don tattauna lamarin da Sakataren gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro yayin da aka jibge jami'ai a yankin.
Duk wani yunkurin jin ta bakin hukumar yan sanda ya ci tura kasancewar kakakin yan sandan Bauchi, SP Ahmad Wakil bai ɗaga kiran waya ba.
Wani mazaunin Alkaleri da ya nemi a sakaya bayanansa ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa matsalar tsaro ta fara yawaita a yankin, yan bindiga na yawan ɗaukar mutane dan neman fansa.
Ya ce ko wannan harin sun yi kokarin sace mutane amma mutane suka farga suka tare su, ganin ba zasu samu aikata abin da suka zo yi ba sai suka buɗe wuta.
Mutumin, wanda ya tura wa wakilin mu hoton lokacin da aka yi wa mutanen da suka mutu Jana'iza, ya ce:
"Yan bindiga sukayi kokarin shiga yankin da abun ya faru, mutane gari sukayi kokarin hanasu shiga, da suka ga kaman za'a cinmusu sai suka bude wuta inda mutum hudu shuka rasu nan take."
A wani labarin kuma Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook
ta ɗaure wani mutumi na tsawon wata biyu a gidan Gayaran hali bayan kama shi da laifin yaɗa ƙarya kan COVID19 a Facebook.
Mutumin mai suna, Habibu Rabiu, ya yi wani rubuta inda ya ankarar da mutane cewa rasa rayuka na ƙaruwa a Kogi sanadiyyar zazzaɓi.
Asali: Legit.ng