Yan Najeriya sun yi ca kan wani lauya da ya ce mai gidan haya ba zai ƙara kuɗi ba da sai izinin 'yan haya

Yan Najeriya sun yi ca kan wani lauya da ya ce mai gidan haya ba zai ƙara kuɗi ba da sai izinin 'yan haya

  • Wani lauya a Najeriya ya haddasa cece-kuce yayin da ya yi ikirarin cewa masu gidajen haya ba su da ikon ƙara kudi sai yan haya sun amince
  • Lauyan mai suna @Egi_nupe_ ya ce idan mai gidan ya matsa sai ya ƙara kuɗin ba tare da yarjejeniya ba, masu haya su nemi gargaɗin tashi
  • Amma rubutun shi a Tuwita ya jawo zafafan martani daga yan Najeriya, mafi yawa na ganin ba zai taɓa yuwuwa a Najeriya ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani rubutu a Tuwita da ya watsu wanda wani lauya ɗan Najeriya ya yi game da ƙara kuɗin haya da masu gidaje ke yi ya harzuƙa mutane da dama.

Lauyan mai shafin @egi_nupe_ ya yi ikirarin cewa mai gidan haya ba shi da ikon karawa kwastumansa kuɗi ba tare da sun zauna sun yi yarjejeniya da farko ba.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

Lauya ya jawo cece kuce.
Yan Najeriya sun yi ca kan wani lauya da ya ce mai gidan haya ba zai ƙara kuɗi ba sai izinin 'yan haya Hoto: @Egi_nupe_.
Asali: Twitter

Lauyan ya rubuta a shafinsa cewa:

"Mai gidan da kuke haya bai da ikon kara kuɗin haya ba tare da sanin ku ba, dole kowane ɓangare ya amince. Idan ya matsa, ku nemi ya baku sanarwan gargaɗin tashi. Bayan wa'adin gargaɗin ya kare Kotu ce kaɗai zata iya tashin ku daga gidan."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duba abin da ya rubutu anan;

Maganar ta jawo cece-kuce

Sai dai wannan zancen na lauya ya ja hankalin yan Najeriya da dama suka tofa albarkacin bakin su, da yawa na ganin da wuya a iya yi wa masu gidajen haya haka a Najeriya.

Da yawan waɗan suka faɗi ra'ayoyin su sun bayyana yadda suka kwashi yan kalo da masu gidajen da suke haya.

@dozierocks ya ce:

"Ya maka daɗi ka faɗi haka. Ka gina kadara da kudaɗen da ka sha gumi ka nema tsawon shekaru don ka zuba yan haya da nufin ka dogara da abun da zaka samu idan Fansho ya gaza maka amma kuma masana su tunkare ka da irin kalaman nan. Gaskiya ina da tabbaci kana haya ne a Legas."

Kara karanta wannan

Insha Allahu zamu kubutar da duk mutanen da aka sace, da yuwuwar mu sake rufe layukan waya, Gwamnan Arewa

@Efemena_IK ya ce:

"Idan ka mallaki kadara irin haka zaka so wani ya yi maka ƙarfa karfa kan abinda ka wahala? Kai abu ba naka ba don me zaka yi ikirarin kwacewa? Ka yi kokarin gina naka gidan ya fi ka fake da matsala don kin biyan kuɗin haya. A hankalce wannan ba dai-dai bane."

@Basil_Uka ya ce:

"To ya zaka yi idan ya yi amfani da marasa kunyar Anguwa su yi masa maganinka?"

A wani labarin kuma Babbar Nasara: Cikakken jerin sunayen kwamandojin yan ta'adda sama da 20 da Sojoji suka aika lahira

Ƙungiyar ta'addanci ISIS ta fitar da cikakken jerin kwamandojin mayaƙan ISWAP da gwarazan sojoji suka samu nasarar tura su barzahu su haɗu da Allah.

Sojojin Najeriya tare da haɗin guiwar rundunar sojin ƙasa da ƙasa sun ragargaji yan ta'addan a wani gumurzu da suka yi makonni kalilan da suƙa shuɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel