Sufuri: Tashin hankali yayin da injin jirgi ya kama da wuta a sama, ya sauka a filin jirgin Murtala

Sufuri: Tashin hankali yayin da injin jirgi ya kama da wuta a sama, ya sauka a filin jirgin Murtala

  • An samu tashin hankali yayin da wani jirgin sama ya samu tasgaro a sama a wani yankin jihar Legas
  • An ruwaito cewa, jirgin ya samu matsala, inda wani injinsa ya kama da wuta yayin da yake shirin sauka a Legas
  • Hakazalika, an ce fasinjoji sun sauka lafiya, kuma ba su shiga wani tashin hankali ba, kana an ba su hakuri

Legas - An dakile wani babban hatsarin jirgin sama a lokacin da wani jirgin sama na Overland Airways ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas daga filin jirgin sama na Ilorin a jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba inda daya daga cikin injunan jirgin ya kama wuta a sama a lokacin da jirgin ke tunkarar filin jirgin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Injin jirgin Overland ya kama da wuta a Legas
Sufuri: Tashin hankali yayin da injin jirgi ya kama da wuta a sama, ya sauka a filin jirgin Murtala | Hoto: wikimedia.org
Asali: UGC

Fasinjoji 33 dake cikin jirgin sun sauka lafiya a sashen filin jirgin sama na kasa da kasa.

An samu labarin cewa Matukin Jirgin na ATR-42 ya ayyana 'May Day' wanda a lafazin sufurin jiragen sama ke nuni da halin neman taimakon gaggawa yayin da hukumomi a filin jirgin suka tanadi dukkan matakan gaggawa yayin da ma’aikatan ke kokarin sarrafa jirgin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce fasinjojin sun natsu a lokacin da ake gudanar da aikin ceton.

Kamfanin ya ce:

“Overland Airways na son sanar da jama’a cewa jirginsa OF1188 daga Ilorin zuwa Legas ya gamu da wani yanayi mai zafi da ba a saba gani ba a daya daga cikin injunansa a yau Laraba 15 ga watan Yuni, 2022 da misalin karfe 7:50 na dare.

Kara karanta wannan

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

"Wannan ya faru ne a lokacin da jirgin ke gab da sauka kuma jirgin ya sauka lafiya yayin da ma'aikatan jirgin suka aiwatar da dabarar tsarinsu kan irin wannan yanayi mara kyau."

Hakazalika, kamfanin ya kuma ba fasinjoji hakuri bisa rashin jin dadin da aka samu, sannan ya ce zai kula da dakile faruwar hakan a nan gaba.

Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kamaru

A wani labarin, wani jirgin sama mai ɗaukar Fasinjoji ya yi haɗari a kusa da babban birnin kasar Kamaru, Yaounde ranar Laraba, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, ma'aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar, ta bayyana cewa karamin jirgin saman dake ɗauke da mutane 11 ya yi hatsari ne a wani daji dake Kudu da Yaounde.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzun ba'a gano musabbabin da ya yi sanadin hatsarin ba, amma wasu bayanai sun bayyana cewa sadarwa ce da datse tsakanin matukin da kuma filin jirgi.

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.