Yan Bindiga Sun Bi Tsohon Kwamishina Har Gidansa Sun Sace Shi a Adamawa, Sun Bindige Mutum 2 Har Lahira
- Wasu yan bindiga sun kai hari gidan tsohon kwamishinan ma'aikatar Gidaje da Tsara Birane, Injiniya Babangida a garin Girei, Jihar Adamawa.
- Bayan sun yi wa gidansa kawanya, yan bindigan sun kutsa sun harbe shi a kafarsa sannan suka yi awon gaba da shi
- Wani cikin yan uwan tsohon kwamishinan ya tabbatar da harin ya kuma ce wadanda suka sace shi sun bukaci N30m a matsayin kudin fansa
Jihar Adamawa - Wasu yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Gidaje da Tsara Birane, Injiniya Babangida a gidansa da ke Adamawa a ranar Talata.
An rahoto cewa wadanda suka sace shi sun zagaye gidansa da ke kauyen Bajabire a karamar hukumar Girei na jihar sannan suka harbe shi a kafa, Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan bindigan sun kuma kashe wasu mutane biyu sun kuma raunata wasu da dama kafin suka sace tsohon kwamishinan.
Dan uwan tsohon kwamishinan ya magantu
Wani dan uwan tsohon kwamishinan ya shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun nemi a biya Naira miliyan 30 don fansarsa.
Abin damuwar shine yayin zaben fidda gwani na APC da ya gabata, da kyar ya sha yayin da wasu suka kai masa hari suka fasa gilashin motarsa," a cewar wani dan uwansa da ya bukaci a sakaya sunansa.
Yan sanda sun yi martani
Rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakinta SP Suleiman Nguroje ta ce ta samu rahoton afkuwar lamarin.
Ya kara da cewa suna daukan matakan ganin sun ceto wanda abin ya ritsa da shi.
Katsina: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari, Sun Bi Gida-Gida Sun Sace Maza 6 Da Matar Aure Da Yarta
A wani rahoton, wasu yan bindiga sun kai hari a garin Shola a karamar hukumar Katsina ta Jihar Katsina, inda suka sace mutane takwas yayin harin.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Channels Television ta wayar tarho cewa yan bindigan a kan babura sun afka wa garin ne a safiyar ranar Talata.
Channels Television ta lura cewa garin wanda ke bayan sabon ginin da aka mayar Asibitin Koyarwa Na Tarayya ta Katsina yana fuskantar barazana daga yan bindigan ne saboda kusancinsa a garin Bugaje a karamar hukumar Jibia inda yan bindiga suka yi kaka-gida.
Asali: Legit.ng