Wutar Lantarkin Najeriya ta Lalace, Daga 3,703MW An Koma Samun 9MW, FG
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da lalacewar wutar lantarkin kasar nan a ranar Lahadi da ta gabata da asubahi
- An gano cewa, wutar ta kai kololuwar 3,703MW da safiyar Lahadi wurin karfe 5 amma zuwa yammaci ta lalace inda ta ke iya bada 9MW
- A halin yanzu, injiniyoyi suna aikin gyaranta inda suka kai ga farfado da 2,744.6MW a ranar Litinin da ta gabata
A ranar Litinin, Bangaren tsarin samar da wutar lantarki ta Najeriya, wani sashi na kamfanin rarrabe wutar lantarki na gwamnatin tarayya, ya nuna cewa wutar lantarkin kasar nan ta lalace a ranar Lahadi inda ta koma samar da wuta mai yawan 9MW daga 3,703MW.
Najeriya tana fuskantar rashin wutar lantarki tun daga ranar Lahadi bayan wutar ta lalace wurin karfe 6 na yammaci, kafin injiniyoyin Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki na Najeriya su yi kokarin farfado da ita.
A rahoton jaridar Punch na ranar Litinin, lalacewar wutar lantarkin na ranar Lahadi shi ne kashi na biyar a shekarar 2022, lamarin da yasa kamfanonin rarrabe wutar lantarkin masu yawa suka rufe.
Bayanan da aka samu daga NESO a ranar Litinin a Abuja, wanda ya bayyana yawan wutar lantarkin da ake samu a ranar Lahadi, ya nuna cewa an kai 3,703MW wurin karfe 5 na asuban Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma hakan ya tabarbare inda ya koma 9MW wurin karfe 7 na yammacin Lahadin, lamarin da ya tabbatar da lalacewar wutar lantarkin kasar.
Kamfanonin Rarrabe Wutar lantarki da suka hada da na Enugu, Abuja, Kaduna da sauransu sun tabbatar da lalalcewar wutar lantarkin a sakonnin da suka tura a daren Lahadi.
Duk da babu bayani daga TCN, amma an gano cewa gyaranta a ranar Litinin ya yi nisa inda ya kai 2,744.6MW wurin karfe 6 na safiyar Litinin.
Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta kai ga lalacewar wutar Ƙasa, FG
A wani labari na daban, Ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a ranar Asabar ta ce lalacewar wutar lantarkin kasar nan ya biyo bayan barna da ake yi wa kasar a hasumiyar rarrabe wutar lantarkinta.
TheCable ta ruwaito cewa, wutar Najeriya ta lalace a ranar Juma'a, karo na uku a cikin makonni kadan, lamarin da ya jefa wasu jihohin kasar cikin matsalar wutar lantarki.
Da farko da, ma'aikatar wutar lantarkin ta ce tana bincikar dalilin lalacewar wutar kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng