Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta kai ga lalacewar wutar Ƙasa, FG

Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta kai ga lalacewar wutar Ƙasa, FG

  • Ma'aikatar wutar lantarki ta kasa ta ce barna da ake mata a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ke janyo lalacewar wutar kasar nan
  • Kamar yadda ta fitar da sanarwa ga jama'ar kasar nan, ta ce a kwantar da hankali domin kuwa gwamnatin tarayya na kokarin shawo kan lamarin
  • Ta sanar da yadda aka rasa 400MW na wutar lanarki sakamakon barna da aka yi a masomin wutar lantarki na Odukpani Ikot Ekpene

FCT, Abuja - Ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a ranar Asabar ta ce lalacewar wutar lantarkin kasar nan ya biyo bayan barna da ake yi wa kasar a hasumiyar rarrabe wutar lantarkinta.

TheCable ta ruwaito cewa, wutar Najeriya ta lalace a ranar Juma'a, karo na uku a cikin makonni kadan, lamarin da ya jefa wasu jihohin kasar cikin matsalar wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa

Da farko da, ma'aikatar wutar lantarkin ta ce tana bincikar dalilin lalacewar wutar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta ka ga lalacewar wutar Ƙasa, FG
Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta ka ga lalacewar wutar Ƙasa, FG. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC
"Karin bayani kan takarda da muka saki ga manema labarai, muna son sanar da jama'a cewa dalilin rashin wutan nan shi ne ayyukan mabarnata masu barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki da ke Odukpani Ikot Ekpene wanda yasa aka rasa 400MW na wutar da ake samu, takardar tace kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan babu bata lokaci ya kawo daina aikin wasu manyan injinan samar da wutar lantarki a fadin kasar nan.

Kamar yadda TVC News ta bayyana, takardar ministan ya fitar da sa hannun mai bashi shawara na musamman kan lamurran yada labarai, Isa Sanusi:

“Muna sanar da jama'a cewa ana aikin gyaran wutar lantarkin daya bayan daya yayin da sauran injinan ke aiki tare da kokarin rufe gibin rashin wutar da ake fama da shi."

Kara karanta wannan

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

Muna Bincike Kan Dalilin Lalacewar Lantarki Na Ƙasa, In Ji Gwamnatin Tarayya

A wani labari na daban, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana bincike kan lalacewar wutar lantarki na kasa, rahoton Daily Trust.

Wutar lantarkin na kasa ya lalace ne a ranar Juma'a, hakan ya jefa kasar cikin duhu. Amma, cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Makamashi ta fitar, ta ce tana aiki domin ganin an gyara matsalar.

Ta ce Hukumar Kula Da Lantarki na Kasa, NERC, mai kula da lantarkin na kasa, tana kan aikin ganin cewa an dawo da lantarkin.

"Muna son mu sanar da al'ummar kasa cewa an samu lalacewar wutar lantarki na kasa wanda ya faru misalin ƙarfe 1830hrs a ranar 8 ga watan Afrilun 2022, wanda hakan ya janyo rashin wuta a sassa daban-daban na kasar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng