Jirgin Shugaba Buhari zai sake lulawa zuwa kasar Rwanda don halartan wani muhimmin taro
- Jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai daga zuwa kasar Rwanda domin halartan taron shugabannin kungiyar Commonwealth na 2022
- Shugaba Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa wannan babban taron ne a cikin mako mai zuwa
- Stanislas Kamanzi, babban kwamishinan Rwanda a Najeriya ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da aka gudanar a babbar birnin tarayya Abuja
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kasashe rainon Ingila wato Commonwealth na 2022 wanda aka shirya gudanarwa a Kigali, kasar Rwanda, a mako mai zuwa.
Stanislas Kamanzi, babban kwamishinan Rwanda a Najeriya ne ya bayyana hakan a wajen taron sada zumunta na kafin taron na CHOGM 22 da aka gudanar a Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari
Ya ce:
“Kasar Rwanda da mutanenta sun shirya karbar bakuncin daya daga cikin manyan tarukan duniya tare da manyan shugabanni da tawagoginsu da za su hallara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abin farin ciki ne a gareni na mika godiya ga gwamnatin tarayyar Najeriya musamman ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amsa gayyatar da shugaba Paul Kagame ya yi masa da kuma muhimmiyar tawagar da zai jagoranta zuwa Kigali."
Kamanzi ya bayyana cewa taron zai zama wani dandalin muhawara da daukar matakai kan batutuwan na gama gari, wadanda suka hada da: shugabanci da bin doka; kiyayewa tare da alaka tsakanin tattalin arziki da muhalli; lafiya; fasaha da matasa.
Babban kwamishinar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta ce a yanzu Birtaniya a shirye take ta mika wa kasar Rwanda shugabar kungiyar Commonwealth bayan shekaru hudu.
Kwankwaso: Ni zan magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan mulkin APC
A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar idan ya zama shugaban kasa.
Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba, Leadersip ta ruwaito.
Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.
Asali: Legit.ng