Yan bindiga sun sace wani malamin addini da matarsa, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansa

Yan bindiga sun sace wani malamin addini da matarsa, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansa

  • Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da limamin cocin Anglican na Jebba, jihar Kwara, Rt. Rev. Aderogba
  • An sace Aderogba, matarsa da kuma direbansa ne a hanyar babban titin Oyo/Ogbomoso a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni
  • An tattaro cewa maharan sun tuntubi yan uwan mutanen inda suka bukaci a biya naira miliyan 50 kudin fansarsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo – Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da Limamin cocin Anglican na Jebba da ke jihar Kwara, Rt. Rev. Aderogba, matarsa da kuma direbansa a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni a babbar hanyar Oyo/Ogbomoso.

Jaridar Punch ta rahpoto cewa malamin addinin da matarsa na hanyarsu ta zuwa jihar Kwara ne lokacin da motarsu ta baci a wani wuri da babu mutane da misalin karfe 8:30 na dare.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

Ba a jima ba sai ga yan bindigar sun farmake su sannan suka tisa keyarsu zuwa cikin jeji.

Jami'an yan sanda
Yan bindiga sun sace wani malamin addini da matarsa, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Majiyoyi sun bayyana cewa wadanda suka sace su sun bukaci a biya naira miliyan 50 domin su sake su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da sace mutanen a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Litinin kuma ya ce jami’ansu sun shiga aiki don ceto su da kuma kama masu laifin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Sanarwar ta ce:

“A ranar Lahadi 12/06/2022 da misalin karfe 21:00, wani Rev. Adekunle Adeluwa ya kaiwa rundunar rahoto a hedkwatarta ta Atiba, garin Oyo cewa da misalin karfe 20:30, an sace wani Limamin Anglican, Rt. Rev Aderogba na Jebba, jihar Kwara tare da matarsa da direbansa.
“Binciken farko ya nuna cewa motar wanda aka sacen ya samu matsala yayin da suke tafiya daga Yewa, jihar Ogun zuwa Jebba, jihar Kwara a wani wuri da babu mutane a hanyar babban titin Oyo/Ogbomoso.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

“Mataimakin kwamishinan yan sanda da ke kula da ayyukan rundunar shi ke jagorantar aikin ceto su kuma tuni ya tsunduma aiki a ranar Lahadi 12/06/2022.
“Dukannin tawagar dabaru na rundunar tare da maharba da yan banga sun shiga aikin ceto mutanen.”

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi, a jihar Anambra.

An tattaro cewa an kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

An tattaro cewa an sace shugaban matasan ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki gidansa da ke garin Ukpor.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng