Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bada Hutun Ranar Demokradiyya Na 2022

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bada Hutun Ranar Demokradiyya Na 2022

  • Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 13 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu don bikin Ranar Demokradiyya na bana
  • Rauf Aregbesola, Ministan Harkokin Cikin Gida ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis
  • Ministan ya bukaci yan Najeriya su yi amfani da bikin don waiwaye kan sadaukarwa da mazan jiya suka yi wa Najeriya don ganin ta cigaba da zama a matsayin kasa daya cikin aminci da tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litnin 13 ga watan Yunin 2022, a matsayin ranar hutu, domin bukin ranar Demokradiyya na wannan shekarar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da ya raba wa kafafen watsa labarai a ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Kungiyar ISWAP Ne Suka Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bada Hutun Ranar Demokradiyya Na 2022
FG Ta Bada Hutun Ranar Demokradiyya Na 2022, Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya taya yan Najeriya murnar bikin ya kuma bukaci dukkan yan kasar su mara wa gwamnati mai ci yanzu baya don tabbatar da tsaro da hadin kai da cigaba a kasar.

"A yayin da muke bikin wata Ranar Demokradiyya a tarihin kasarmu, mu dauki lokaci mu yi waiwaye kan kokarin da mazan jiya suka yi don tabbatar da hadin kan Najeriya a matsayin kasa daya, mai tsaro da hadin kai.
"Da kallubalen da muke fuskanta a Najeriya a yau. Abin da na gani shine damar mu fuskanci gaskiya, mu fahimci juna, mu girmama juna mu zauna lafiya da cigaba a maimakon rabuwa," in ji Aregbesola.

Ministan ya kuma shawarci yan Najeriya su yi amfani da manhajar inganta tsaron cikin gida na (N-Alert) da aka kirkira don inganta tsaro da kare iftila'i.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Ya bada tabbacin cewa kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na tabbatar tsaro da kawo cigaba da daidaita tattalin arziki, kasar za ta cigaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel