An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

  • Rahotanni sun kawo cewa mutane da dama sun raunana a ranar Asabar da safe bayan wani rikici ya barke tsakanin ‘yan kasuwa Hausawa da Inyamurai
  • Lamarin ya afku ne a sabuwar kasuwar Benin da ke jihar Edo, bayan wani Inyamuri ya nemi wani Bahaushe ya bar masa gaban shagonsa
  • An ce Bahaushen ne ya caki Inyamurin kan haka, lamarin da ya fusata matasa har suka far masa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - An samu barkewar rikici a safiyar ranar Asabar, 11 ga watan Yuni a garin Benin, jihar Edo, yayin da fusatattun matasa wadanda yawancinsu yan kasuwa ne a sabuwar kasuwar Benin suka tashi hankali bayan wani dan kasuwa daga arewa ya farma takwaransa na Igbo da adda.

Rigima ya fara ne bayan wani dan sabani da ya shiga tsakanin yan kasuwar biyu. An ce dan Igbon ya umurci Bahaushen da ya bar masa gaban shagonsa, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsageru sun sace mai daukar hoton gidan gwamnatin jiha, suna neman N50m

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo
An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo Hoto: Punch
Asali: UGC

An tattaro cewa ana haka ne sai Bahaushen dan kasuwan wanda hakan bai yi masa dadi ba ya zaro addansa sannan ya caki Inyamurin.

Wani bidiyo da ke yawo a shafin soshiyal midiya ya nuno fusatattun matasan suna zanga-zanga yayin da suka farma wanda ake zargi da aikata kisan kan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa tawagar tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojoji da yan sanda sun karbe yankin da lamarin ya afku.

Mafarauta sun kashe uwa da danta kan zargin maita a Adamawa

A wani labari na daban, mun ji cewa Mafarauta sun harbe wata mata mai suna Uzarai Muda da danta Klandang Musa, mazauna yankin Bitikaya da ke karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa kan zarginsu da maita.

An zargi wadanda abun ya ritsa da su da kashe mutane tare da daura ma mazauna yankinsu ciwo tsawon shekaru da dama, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

Domin raba garinsu da maitancinsu, sai wasu yan doka biyu a garin, Hassan Solomon mai shekaru 26 da Uleri Shaba mai shekaru 28 dukkansu yan garin Gulak suka harbe uwa da dan, inda suka mutu a nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng