Mafarauta sun kashe uwa da danta kan zargin maita a Adamawa

Mafarauta sun kashe uwa da danta kan zargin maita a Adamawa

  • Mafarauta sun kashe wata mata mai suna Uzarai Musa da danta kan zargin su da maita a jihar Adamawa
  • Sun yi zargin cewa mamatan sune ke kashe mutane a yankin tare da daurawa wasun su ciwo tsawon shekaru da dama
  • Sai dai an kama wasu mutane 15 kan haka yayin da rundunar yan sanda ta ce ba za ta yarda da daukar doka a hannu ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - Mafarauta sun harbe wata mata mai suna Uzarai Muda da danta Klandang Musa, mazauna yankin Bitikaya da ke karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa kan zarginsu da maita.

An zargi wadanda abun ya ritsa da su da kashe mutane tare da daura ma mazauna yankinsu ciwo tsawon shekaru da dama, Leadership ta rahoto.

Mafarauta sun kashe uwa da danta kan zargin maita a Adamawa
Mafarauta sun kashe uwa da danta kan zargin maita a Adamawa Hoto: Leadership
Asali: UGC

Domin raba garinsu da maitancinsu, sai wasu yan doka biyu a garin, Hassan Solomon mai shekaru 26 da Uleri Shaba mai shekaru 28 dukkansu yan garin Gulak suka harbe uwa da dan, inda suka mutu a nan take.

Kara karanta wannan

Firgici: An cafle mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

Mafarautan sun yi ikirarin cewa mayun da aka kashe sun halaka yan uwansu biyu sannan sune ke da alhakin wasu mace-mace masu ban mamaki da abubuwan da ke faruwa a garinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mafarautan sun harbi marigayiya Uzarai a ciki, yayin da suka harbi danta a wuya a gidansu.

A halin da ake ciki, jami’in da ke kula da Crack Squad na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, CSP Ahmed Danjuma Gombi, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da hannu a kisan mutanen biyu kuma ana ci gaba da bincike a kansu.

Ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya idan aka same su da laifi domin ‘yan sanda ba za su yarda da daukar doka a hannu ba, Daily Post ta rahoto.

'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan bindiga 'A jirgin Helikwafta' sun halaka dandazon mutane a Kaduna

A wani labarin, Yan bindiga sun yi awon gaba da wani shugaban matasa a ƙaramar hukumar Ihialia da ke jihar Anambra, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya a yankin ta bayyana cewa bayan sace shugaban matasan, maharan sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukuma suka kwashi motoci masu darajar miliyoyin kuɗi da aka tanada son tallafawa mutane.

Shugaban ƙungiyar cigaban matasa ta Okija, Kwamaret Ononuju Maxwell Chigozie, a wata sanarwa ya ce mazauna yankin sun shiga ƙunci sanadiyyar harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel