Yadda Mahaifinmu Ya Mika Kansa Ga Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ya Cece Mu, Hajiya Asheku

Yadda Mahaifinmu Ya Mika Kansa Ga Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ya Cece Mu, Hajiya Asheku

  • Hajiya Asheku, yar marigayi Zakari Umaru Kigbu, ta magantu kan yadda yan bindiga suka halaka tsohon kwamishinan na NPC a gidansa
  • Asheku ta ce misalin karfe 11 na dare maharan suka shigo gidansu amma suka kashe balle kofan shiga dakin mahaifinta, don haka sai suka fara neman yara a gidan
  • Umaru Kigbu ya fito daga dakinsa ne ya fuskanci yan bindigan a lokacin da ya lura sun gano yaransa a bandaki kuma suka ta kokarin harbe su don ya ki fitowa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nasarawa - A ranar 28 ga watan Maris ne wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari gidan tsohon kwamishinan kidaya da kasa, NPC, Zakari Umaru Kigbu, suka kashe shi, sannan suka sace dansa da kanwar matarsa.

Kafin a kashe shi, Kigbu mai shekaru 60 da haihuwa kuma tsohon sojan saman mai ritaya yana koyarwa ne a kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai a Lafia, (IMAP).

Kara karanta wannan

Dan shekara biyu ya bindige mahaifinsa har lahira yayin wasa da bindiga a Amurka

Yadda Mahaifina Ya Mika Kansa Ga Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ya Cece Mu, Hajiya Asheku
Mahaifina Ya Mika Kansa Ga Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ya Cece Mu, Hajiya Asheku. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da yan uwa da abokan arziki ke cigaba da jimamin rashinsa, yarsa mai shekara 29, Hajiya Asheku, cikin hawaye ta bada labarin yadda makasan suka kashe mahaifinta, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Asheku ta ce:

"Ni ne ta biyar cikin yayan Zakari Umaru Kigbu kuma yarsa mace tilo.
"A ranar da abin ya faru, ina zaune a falo a gidanmu da mahaifina da mahaifiyata da yan uwa na muna kallon wani shiri a talabijin.
"Yayin da muke kallon talabijin din, mahaifina da mahaifiyana sun shiga dakinsu sun kwanta. Wasu cikin yan uwana suma sun tafi sun kwanta, saboda abin ya faru ne misalin karfe 11 na dare.
"An bar ni a falo tare da dan uwa ne wanda ke tura wasu abubuwa daga kwamfutarsa.
"Kwatsam sai muka ji harbin bindiga. Daya cikin yan uwan mu ya yi maza ya rufe kofar kitchen da ta bulle tsakar gida.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

"Wasu daga cikin mu mun ruga dakin mahaifinmu don mu boye wasu kuma suka shiga dakin mahaifiyar mu.
"Bata garin, dauke da bindigu, sun balle kofar gidan mu suka nufo dakin mahaifin mu.
"Da mahaifin mu ya lura dakinsu za su zo, sai ya umurci dukkan mu mu fita mu tafi store mu boye.
"Maharan sun yi kokarin balle kofarsa amma suka kasa saboda kofar na da karfi, sai suka fara neman mu."

Asheku ta cigaba da cewa:

"Da muka lura za su iya ganin mu cikin sauki a store, sai muka tafi bandakin mahaifyar mu muka boye muna adduar Allah ya kawo mana dauki.
"Sun ta neman mu amma ba su gan mu ba.
"Suna cikin neman mu sai suka ji muna kus-kus a cikin bandaki.
"Sun umurci mu fito ku su balle kofar su harbi dukkan mu.
"Saboda muna jin tsoro sai muka ki fitowa sai suka umurci abokansu da ke waje su harbe mu ta tagar bandaki.

Kara karanta wannan

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

"Suka fara harbe-harbe amma ba su same mu domin duk mun kwanta.
"Ana hakan, mahaifinmu yayi kokarin kiran yan sanda da sojoji amma bai samu amsa mai gamsarwa ba.
"Don haka, ba shi da wata zabi sai ya fito daga dakinsa domin ya kare mu, a lokacin ne suka harbi mahaifi na.
"Da muka ji karar harbin bindigan, dukkan mu mun fito waje muka gan shi kwance cikin jininsa."

Asheku ta ce maharan su hudu ne kuma bata san ko harin na da alaka da siyasa ba.

Ta ce mahaifinta na harka da yan siyasa amma ba ta san dalilin da yasa aka kawo masa harin ba, rahoton The Nation.

"Da suka zo, sun ce ba za su tafi ba sai sun kashe mahaifina a daren.
"Da suka harbe shi, dukkan mu mun fito mun gan shi cikin jini amma bai iya magana ba domin ya galabaita. Ya rasu bayan yan mintuna," ta kara da cewa.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci, An Fara Bincike

Asheku ta ce mahaifinta mutumin kirki ne kuma mai saukin hali wanda ke kula da su da sauran yan uwansa.

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

A wani rahoton, Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda zasu cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Gwamnan ya kwatanta tubar mayakan Boko Haram da ISWAP fiye da 35,000 a matsayin taimako daga Ubangiji sakamakon addu’o’in mutane daban-daban na duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel