Zamfara: Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Zamfara: Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mutanen Jihar Zamfara sun shiga zaman makoki bayan rasuwar babban sarki a jihar
  • Hakan na zuwa ne bayan rasuwar Sarkin Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu bayan fama da rashin lafiya
  • Marigayi Ahmad Umar shine sarki wanda ya fi dadewa a kan gadon sarauta a Zamfara inda ya shafe shekaru 61

Jihar Zamfara - Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da rasuwar Sarkin Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu na Jihar, Alhaji Ahmad Umar.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Kabiru Balarabe ya sanar kuma wakilin Legit.ng na Zamfara, Jamilu Ibrahim ya aiko da shi, sarkin ya rasu da rana bayan fama da rashin lafiya.

Zamfara: Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta a Zamfara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya. Hoto: Photo credit: Lawali Muhammad.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

PDP: Tsohon Ministan Jonathan Ya Ci Zaben Fidda Gwanni Na Sanata a Jigawa

Marigayi Ahmad Umar shine sarki wanda ya fi kowa dadewa kan gadon sarauta a Jihar Zamfara, an nada shi sarki ne a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1961.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel