Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka matar basarake, sun sace 'yan biki

Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka matar basarake, sun sace 'yan biki

  • 'Yan bindiga sun halaka matar wani basarake, tare da awon gaba da 'yan biki a Sakkwoto, gabashin yankin jihar dake makwabtaka da jihar Zamfara da Nijar
  • An tattaro yadda maharan suka halaka matar basaraken bayan ta ki bin su maboyarsu gami da yin garkuwa da mutane 50 tare da raunata 'yan biki da dama a Gebe
  • Har ila yau, sun shiga kauyen Alkammu inda suka yi garkuwa da mutane bakwai duk da wani basarake tare da sace wasu shanun kauyen

Sokoto - 'Yan bindiga sun halaka matar wani basarake gami da raunata mutane da dama a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwoto a harin da suka kai a tsakar ranar Asabar.

An samu labarin yadda suka yi awon gaba da mutane hamsin da bakwai daga kauyuka biyu - Gebe da Alkammu. 50 daga Gebe yayin da suka yi garkuwa da bakwai daga Alkammu.

Kara karanta wannan

Guje wa Kamen EFCC: 'Yar Kasuwa ta Sheka Lahira Bayan ta Garkame Kanta a Bandaki

Premium Times ta tattaro yadda 'yan bindigan suka halaka matar sarkin kauyen Gebe bayan sun shiga gidan biki.

Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka matar basarake, sun sace 'yan biki
Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka matar basarake, sun sace 'yan biki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Leadership ta rahoto cewa, wata majiya, wacce ya bukaci a sakaya sunanta don tsaro ta ce, ga dukkan alamu 'yan bindigan sun ga yadda 'yan bikin ke kai komo daga wasu garuruwa zuwa Gebe.

"An yi shagalin wani biki jiya a gidan sarkin kauyen.Yawancin wadanda aka yi garkuwa da su sun zo ne daga cikin garin Sakkwoto da Isa wadanda suka zo yankin don taya basaraken murna," a cewarta.

Majiyar ta bayyana yadda aka halaka matar basaraken saboda yadda ta ki yarda a yi garkuwa da ita.

"A iya sanin mu, ita kadai aka halaka. Sannan mutanen kauyen sun shaida min yadda ta ce wa 'yan bindigan ba za ta bi su mabuyarsu ba. Kuma sun raunata mutane da dama a farmakin da suka kai saboda sun fara harbe-harbe a lokacin da suka shigo Gebe don su razana mutane."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Osinbajo da Sauran 'yan Takarar APC na Kudu Maso Yamma Sun Sanya Labule

Nuhu Shehu, wani majiya, ya ce sarkin kauyen Gebe ya tabbatar da yadda aka yi awon gaba da mutane 50.

"Ka san tunda babu sabis din waya, zai yi wuya a yi hanzarin kawo dauki. Saboda haka, sai da suka zo Sakkwoto ko Wurno ne muka san abun da ke faruwa. A nan ne muka samu labarin yadda aka yi garkuwa da mutane 50 mafi yawansu daga Sakkwoto da Isa, wadanda suka halarci bikin gami da halaka matar sarkin kauyen," a cewarsa.

Haka zalika, an kai hari yankin Alkammu na karamar hukumar Wurno a daren Juma'a inda suka yi awon gaba da mutane bakwai duk da mai anguwar yankin.

Yusuf Gidan Dare, wani 'dan jaridar yankin ya shaidawa Premium Times yadda maharan suka sace wasu shanu a kauyen.

"Basu halaka kowa ba a harin da suka kai na Alkammu," a cewar Gidan Dare.
"Amma sun yi garkuwa da mazauna kauyen bakwai duk da Dangaladiman Alkammu (wani mai rike da babban mukamin gargajiya) da wasu shida. Na gano yadda har yanzu basu tuntubi iyalansu ba don biyan kudin fansa," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance

A wani labari na daban, Rabaran Andrew Abayomi, daya daga cikin fastocin majami'ar Katolika ta St Francis ta titin Owa-luwa a Owo da ke jihar Ondo, ya labarta yadda aka kai wa majami'ar farmaki.

Daily Trust ta ruwaito yadda masu bauta da dama suka rasa rayukansu yayin da 'yan ta'adda suka tada bom a majami'ar a safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel