Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro

Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro

  • Babban jigon APC na kasa, Bola Tinubu, ya bayar da tallafin naira miliyan 75 ga mutanen da harin Owo ya ritsa da su da kuma cocin da abun ya faru
  • Mai neman takarar shugaban kasar na APC a zaben 2023, ya kuma yi Allah wadai da kisan rashin imani da aka kaiwa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba
  • Ya kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha da su hada karfi da karfe don inganta tsaro a fadin kasar

Ondo - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin kawo dauki ga wadanda harin Owo ya ritsa da su.

Da yake magana a fadar sarkin Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye a yayin ziyarar jaje da ya kai, Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa bayin Allah da ke tsaka da ibadarsu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Ya bayyana harin a matsayin mugunta da ya zama dole a kawo karshensa, yana mai cewa “babu hurumin irin wannan kiyayya da kashe rayukan da basu ji ba basu gani ba" a kasarmu.

Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro
Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro Hoto: Akoko Today.
Asali: UGC

Yan bindiga sun farmaki cocin Katolika na St. Francis a Owo a ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wadanda yawancin mata da yara ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin ya ziyarci cocin don ganin barnar da aka yi, Tinubu ya yi alkawarin bayar da tallafin naira miliyan 50 ga wadanda abun ya ritsa da su da kuma naira miliyan 25 ga cocin Katolika ta Owo.

Da yake nuna bakin cikinsa kan mummunan al’amarin, Tinubu ya bayyana cewa yankin kudu maso yamma bai taba fuskantar hari mai girma irin wannan ba yana mai cewa abun tsoro ne.

Kara karanta wannan

Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo

Dan takarar shugaban kasar na APC ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha da su yi aiki tare domin karfafa tsaro a fadin kasar nan.

Akeredolu, wanda ya mika godiya ga Tinubu kan dakatar da harkokin kamfen dinsa kasa da awa 24 kafin babban taron APC, ya yi alkawarin gabatar da maharan a gaban doka ko kuma ya kai doka har inda suke, The Eagle ta rahoto.

A tawagar Tinubu zuwa Owo akwai tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, shugaban TETFUND, Kashim Ibrahim-Imam, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Yamma, Cif Pius Akinyelure, tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Nuhu Ribadu da tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Otunba Femi Pedro.

Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo

A gefe guda, tsohon kwamishinan labarai na jihar Ondo, Donald Ojogo, ya bayyana cewa da nakiya aka yi amfani wajen kaddamar da harin cocin Owo da ke jihar.

Kara karanta wannan

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels Tv, Ojogo ya ce yawancin wadanda harin ya ritsa da su sun mutu a yayin da suke kokarin tserewa daga wajen da aka dana bama-baman da aka yi amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng