Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci
- Rahoton da muke samu daga jihar Enugu na bayyana cewa, wasu da ake zargin 'yan IPOB ne sun farmaki motar siminti
- An ce sun banka mata wuta, amma 'yan sanda sun yi nasarar ceto motar daidai lokacin da take ci da wuta
- A halin da ake, rundunar ta ce tana ci gaba da bincike don gano wadanda suka tafka wannan mummunan aiki
Jihar Enugu - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta ceto tare da kashe gobarar da ta tashi a wata babbar mota makare da buhunan siminti a yankin Nsukka na jihar Enugu.
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, sun banka wa motar wuta a yayin da suke aiwatar da kakaba haramtacciyar dokar zaman gida a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin a Enugu cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, a kan titin 9th-Mile-Nsukka-Obollo Afor.
Mista Ndukwe ya ce ba a rasa rai a lamarin ba, kamar yadda rahoton Daily Nigerian ya kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Da sanyin safiyar ranar 6 ga watan Yuni, jami’an ‘yan sanda yayin da suke sintiri na karfafa gwiwa a Nsukka, sun lura da wata babbar motar dakon kaya dauke da buhunan siminti da ke cin wuta a mahadar Beach da ke titin Obollo Afor mai lamba 9-Mile-Nsukka-Obollo Afor.
“Gobarar wacce ta kone kan babbar motar, daga karshe jami’an ‘yan sanda ne suka kashe ta tare da taimakon wasu masu kishin al’umma a yankin.
"Ba a rasa rai ba, yayin da aka tsare bodin motar da buhunan simintin."
Kakakin ‘yan sandan ya ce an fara bincike don gano ainihin musabbabin tashin gobarar.
'Yan bindiga sun shiga Abuja da sanyin safiya, sun sace mutane da dama
A wani labarin, The Guardian ta ce, wasu tsageru da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a safiyar ranar Litinin sun kai hari a jerangiyar gidaje na Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.
Daily Trust ta gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a gidajen ne tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin garin, wanda kawai ya bayyana sunansa da Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga jerangiyar gidajen Genuine katin shiga na Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.
Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci, An Fara Bincike
Asali: Legit.ng