Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo

Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo

  • Tsohon kwamishinan labarai na jihar Ondo, Donald Ojogo, ya yi tsokaci kan harin da yan bindiga suka kai wani coci da ke garin Owo ta jihar
  • Ojogo ya bayyana cewa akwai kwararan hujja da ke nuna maharan sun tayar da bama-bamai kafin suka bude wuta kan masu ibada a cocin
  • Ya ce turmutsitsin da aka samu a lokacin da mutane ke guje ma bam din da aka tayar shine ya yi sanadiyar mutuwar yawancin wadanda lamarin ya ritsa da su

Ondo - Tsohon kwamishinan labarai na jihar Ondo, Donald Ojogo, ya bayyana cewa da nakiya aka yi amfani wajen kaddamar da harin cocin Owo da ke jihar.

A ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki cocin St Francis da ke Owo a jihar Ondo a yayin da suke tsaka da ibada.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo
Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo Hoto: PM News
Asali: UGC

Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels Tv, Ojogo ya ce yawancin wadanda harin ya ritsa da su sun mutu a yayin da suke kokarin tserewa daga wajen da aka dana bama-baman da aka yi amfani da su.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Akwai kwararan hujja da ke nuna cewa an yi amfani da ababen fashewa amma bayan abubuwan fashewar daga bayanan da muka samu a wajen wadanda suka tsira, sun ce yayin da suke guduwa waje, sakamakon bama-baman da aka yi amfani da su a cocin, sai kawai aka yi ta harbin su.
“Don haka, a sakamakon turmutsitsin ne yawancin wadannan mutanen suka mutu.”

Tsohon kwamishinan ya bayyana rashin isar yan sanda wajen faruwar lamarin da wuri a matsayin wanda ba za a taba fahimta ba, yana mai cewa tsakanin ofishin yan sanda da wurin faruwar lamarin tafiyar kilomita biyu ne.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ban yi hatsari ba – Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya magantu

Ya ce domin kare al’ummar kasa yadda ya kamata, dole gwamnatin tarayya ta yarda da bukatar kafa yan sandan jiha, jaridar The Cable ta rahoto.

Ya kara da cewa:

“Ofishin yan sanda mafi kusa da wannan waje kilomita biyu ne. akwai ofishin yan sanda kusa da fadar Olowo, kuma wannan abun ya faru ne kusa da fadar.
“Wadannan yan bindiga sun yi harbi na tsawon fiye da mintuna 20 kuma yan sandan basu zo ba. Wannan ne dalilin da yasa muke bukatar yan sandan jiha.
“Idan har da gaske muna son bin tsarin tarayya ta gaskiya, toh ya kamata kowace jiha ta mallaki yan sandanta domin hana faruwar irin haka.”

Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

A baya mun ji cewa, wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun tayar da cocin Katolika na St Francis a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Kara karanta wannan

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

Rahotanni da ke fitowa sun bayyana cewa masu bauta da dama sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata bayan tashin bam a cocin wanda ke kusa da fadar Olowo na Owo, Channels tv ta rahoto.

An tattaro cewa maharan sun dana bam a cocin inda daga bisani suka bude wuta a kan taron jama’a. Kananan yara na cikin wadanda aka kashe a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng