Yanzu Yanzu: Ban yi hatsari ba – Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya magantu

Yanzu Yanzu: Ban yi hatsari ba – Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya magantu

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo cewa ya yi hatsarin mota a babbar birnin tarayya Abuja
  • Osinbajo ya ce sabanin abun da ake ta yayatawa, sun ci karo ne da wani hatsari a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama don haka sai suka tsaya suka taimaki wadanda abun ya ritsa da su
  • Ya ce jami'an tsaro da tawagar likitocinsa sun kwashi mutanen da abun ya cika da su zuwa asibitin sojoji

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, ya bayyana cewa hatsarin mota bai rintsa da shi ba kamar yadda ake ta rade-radi.

Osinbajo ya bayyana cewa sun ci karo da wani hatsari da aka yi ne a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama don haka sai suka tsaya domin taimakawa wadanda lamarin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Nakiya aka dasa: Tsohon kwamishina ya magantu kan harin coci a Ondo

Yanzu Yanzu: Ban yi hatsari ba – Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
Yanzu Yanzu: Ban yi hatsari ba – Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa jami’an tsaronsa da tawagar likitocinsa sun taimaka wajen kwashe mutanen da suka yi hatsarin daga wajen da lamarin ya afku, sannan suka mika su asibitin sojoji.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hatsarin mota bai ritsa da nib a. ina a kan hanyar zuwa filin jirgin sa, sai muka ci karo da wurin wani hatsari.
“Jami’an tsarona da tawagar likitoci sun taimaka wajen dauke wadanda lamarin ya ritsa da su daga wajen hatsarin.
“An kwashe su zuwa asibitin sojojin sama.”

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

A wani labarin, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya dura jihar Ondo domin jajantawa iyalan wadanda aka kashe a wani babban cocin Katolika na St Francis da ke Owo a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

Kamar yadda wani dan takaitaccen hoton bidiyo da Legit.ng ta samu a shafinsa na Tuwita, Gwamna Rotimi Akeredolu yana tare Tinubu a cikin wata mota inda suka nufi karamar hukumar Owo domin ziyartar wadanda abin ya shafa.

Tinubu ya kai wannan ziyara ne daidai lokacin da jam'iyyar APC ke ci gaba da kokarin shirye-shiryen yin zaben fidda gwani na shugaban kasa da ke gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel