Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun shiga Abuja da sanyin safiya, sun sace mutane da dama
- Wani mummunan labarin da ya karade kasar nan ya bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun shiga Abuja
- Rahotanni sun shaida cewa, 'yan bindigan sun shiga jerangiyar gidaje a Gwarinpa, inda suka sace wasu mutane
- Ya zuwa yanzu, hukumar 'yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za ta ba da bahasin gaskiyar lamarin
Gwarinpa, Abuja - The Guardian ta ce, wasu tsageru da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a safiyar ranar Litinin sun kai hari a jerangiyar gidaje na Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.
Daily Trust ta gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a gidajen ne tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin garin, wanda kawai ya bayyana sunansa da Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga jerangiyar gidajen Genuine katin shiga na Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.
Ya bayyana wa majiya ta wayar tarho cewa ’yan bindigar na dauke da baka, da kibiyoyi, da adduna kuma suna da yawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta shaida cewa lamarin fashi ne ba na garkuwa da mutane ba.
Adeh, mataimakiyar Sufeton ‘yan sanda, ta ce tuni aka tattara ‘yan sanda zuwa wurin domin sanin yadda lamarin ya faru da nemo mafita.
Ta yi alkawarin cewa za a sanar da jama'a abin da ya kamata bayan an gano cikakkun bayanai kan lamarin.
Gakuwa da mutane: 'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a babbar hanyar Kaduna
Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci, An Fara Bincike
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin ta fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi wa masu ababen hawa kwanton bauna a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Haka kuma sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma babura guda hudu wadanda ba a yiwa rajista ba daga hannun ‘yan bindigar a yayin musayar wuta, Daily Trust ta ruwaito.
Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na safe.
Asali: Legit.ng