Gakuwa da mutane: 'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a babbar hanyar Kaduna

Gakuwa da mutane: 'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a babbar hanyar Kaduna

  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana aikin da ta yi kan 'yan bindiga a cikin makon nan, inda ta ragargaji wasu a hanyar Birnin Gwani
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun dasa tarkon mugun nufi ga fasinjoji a kan hanyar
  • Da nufin Allah, 'yan sanda sun gano su, sun yi musayar wuta, inda da dama suka samu raunukan harbin bindiga

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin ta fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi wa masu ababen hawa kwanton bauna a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Haka kuma sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma babura guda hudu wadanda ba a yiwa rajista ba daga hannun ‘yan bindigar a yayin musayar wuta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikici: Tsagerun IPOB sun mamaye makarantu, sun fatattaki dalibai saboda wani dalili

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na safe.

'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari
Kaduna: 'Yan bindiga sun game da fushin 'yan sanda, an ragargaji da dama | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Jami’an rundunar ‘yan sandan Kaduna da ke aiki da shiyya ta Buruku a lokacin da suke sintiri a Udawa kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari sun yi taho-mu-gama da wasu ‘yan bindiga a kokarinsu na aikata mugun nufi a kan fasinjojin da ba su ji ba gani.
“Jami’an ‘yan sanda tare da ’yan banga sun nuna jarumtaka wajen mayar da wuta cikin tsanaki, inda suka yi nasarar dakile harin yayin da suka tilasta wa ‘yan bindigar tserewa da raunuka daban-daban zuwa dajin inda suka bar bindiga AK47 guda daya da kuma babura guda hudu marasa rajista.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Rundunar soji ta magantu kan labarin barnar da 'yan ta'addan Kamaru suka yi a Najeriya

“An kwato kayayyakin ne an kai su ofishin ‘yan sanda na Buruku yayin da ake kokarin gano inda ‘yan bindigan da suka jikkata suke domin fuskantar fushin doka.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yekini A. Ayoku, ya yi kira ga al’ummomin da ke kewayen yankin da su sanya ido ga duk wanda aka gani da raunin harsashi, sannan su kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin daukar mataki cikin gaggawa, inji Tori.ng.

Rikici: Tsagerun IPOB sun mamaye makarantu, sun fatattaki dalibai saboda wani dalili

A wani labarin, an samu tashin hankali yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan IPOB ne suka mamaye makarantu a garin Onitsha da wasu sassan yankin Idemili na jihar Anambra inda suka fatattaki dalibai daga ajujuwa.

An ce ‘yan bindigar sun kuma mamaye kasuwanni da wuraren taruwar jama’a domin fatattakar mutane.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun umarci mutane da su koma gida suna masu cewa yau ne “Ranar Biafra”.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Asali: Legit.ng

Online view pixel