Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

  • Tsagerun yan ta'adda sun tayar da bam a cocin Katolika na St Francis a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo
  • An tattaro cewa mummunan al'amarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da wasu suka jikkata
  • Zuwa yanzu babu cikakken rahoto daga mahukunta kan faruwa lamarin na yau Lahadi, 5 ga watan Yuni

Wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun tayar da cocin Katolika na St Francis a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Rahotanni da ke fitowa sun bayyana cewa masu bauta da dama sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata bayan tashin bam a cocin wanda ke kusa da fadar Olowo na Owo, Channels tv ta rahoto.

An tattaro cewa maharan sun dana bam a cocin inda daga bisani suka bude wuta a kan taron jama’a. Kananan yara na cikin wadanda aka kashe a harin.

Kara karanta wannan

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

Wani ganau, Kehinde Ogunkorode, ya ce lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin yayin da mazauna wadanda abun ya zo masu a bazata suka bazama neman mafaka, The Cable ta rahoto.

Da dumi-dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo
Da dumi-dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo Hoto: The Nation
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shahara Reporters ta rahoto cewa wani shaida ya ce abun da ya tashi bam ne amma ba a san adadin wadanda suka mutu ba tukuna.

Ya ce:

“Na yarda cewa bam ne amma ba a san adadin wadanda suka mutu ba tukuna.”

Wani limamin cocin ya bayyana cewa:

“A yayin da muke shirin kawo karshen bautarmu, sai muka fara jin karar harbi da tashin nakiya. Wasunmu mun rufe kanmu na dan wani lokaci. Da muka fito, sai muka ga gawarwaki a kasa."

An kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibition St Louis da asibitin FMC da ke Owo.

Zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu a harin ba.

Kara karanta wannan

ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo

ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo

A wani labari na daban, mummunan rikici ya kaure tsakanin kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, Boko Haram, wacce ta yi sanadin kashe hatsabibin kwamanda mai suna Ummate Ma, da mayakansa, rahoton Leadership.

An tattaro cewa Ummate Ma, wanda aka fi sani da Muhamma wanda ke da mukamin Khayd (Gwamna) da mayakansa, an kashe su ne a ranar 1 ga watan Yuni lokacin da mayakan ISWAP suka kai wa tawagar Kwamandan hari a Dutsen Mandara a karamar hukumar Gwoza a hanyarsa ta zuwa Kamaru.

A cewar bayanan sirri da Zagazola Makama, Kwararre kan tsaro da yaki da ta'addanci a Tafkin Chadi ya samu daga majiyar sojoji, wacce Leadership ta samu, harin ya yi sanadin musayar wuta na tsawon awa biyu tare da kashe yan Boko Haram da dama.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci, An Fara Bincike

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng