Buhari Zai Sake Tafiya Kasar Waje Awanni Bayan Dawowa Daga Madrid

Buhari Zai Sake Tafiya Kasar Waje Awanni Bayan Dawowa Daga Madrid

  • Awanni bayan dawowa da Madrid, Kasar Spain, Shuagba Muhammadu Buhari zai tafi Ghana domin hallartar taron shugabannin kasashe na ECOWAS.
  • Ana fatan Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya a yau Asabar idan an kammala taron da za a gudanar a fadar shugaban kasar Ghana.
  • Wadanda za su yi wa Buhari rakiya sun hada da Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Kasar Waje; Babagana Monguno, Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro da Shugaban NIA, Ahmed Rufa'i Abubakar

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai sake yin tafiyarsa zuwa kasar waje karo na uku cikin kwanaki takwas.

Shugaban kasar da iyalansa sun hallarci taron kungiyar hadin kan Africa AU ta musamman a Malabo, Equatorial Guinea a ranar 26 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Kwanaki kadan bayan dawowa Najeriya, Buhari ya tafi kasar Spain inda ya kai ziyarar aiki ta kwana uku.

Buhari Zai Sake Tafiya Kasar Waje Awanni Bayan Dawowa Daga Spain
Buhari zai tafi Ghana awanni bayan dawowa daga Spain. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Asabar a shafinsa na Facebook, Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya ce Buhari zai sake wata tafiyar, wannan karon zuwa kasar Ghana.

"Shugaba Muhammadu Buhari a yau Asabar 4 ga watan Yuni zai hallarci taron Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, kan rikicin siyasa na Mali da wasu sassan nahiyar.
"Za a yi taron ne a fadar shugaban kasa a Accra, wacce aka fi sani da Jubilee House, domin bita kan nasarorin da gwamnatin Soja na Mali ne yi don mayar da mulki hannun farar hula.
"Shugabannin kasashen kuma za su yi bita kan halin da aka ciki a Jamhuriyar Burkina Faso da Guinea," in ji Adesina.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya daga Madrid

Mutanen da za su yi wa Buhari rakiya

Adesina ya kara da cewa wadanda da za su yi wa Shugaba Buhari rakiya sun hada da:

"Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Kasar Waje; Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa, NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar."

Ana fatan Buhari zai dawo Najeriya a yau Asabar din da zarar an kammala taron a cewar sanarwar ta Adesina.

Tafiyan na Buhari na zuwa ne a yayin da jam'iyyarsa ta APC ke shirin yin zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa.

Za a yi taron ne daga ranar 6 zuwa 8 na watan Yuni.

Osinbajo Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa

A bangare guda, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana ganawa da a akalla gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar da Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a ofishinsa.

Kara karanta wannan

Buhari ya taso daga Madrid, yana hanyarsa ta dawowa Najeriya

Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a dakin taro na Council Chambers a gidan gwamnati a ranar Talata kafin ya tafi Madrid, Spain.

Hakan kuma na zuwa ne bayan kammala tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da kwamitin John Odigie-Oyegun ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164